Connect with us

WASANNI

Chelsea Ta Saka Victor Moses A Kasuwa

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sanya farashin yuro miliyan 12 kan dan wasanta Victor Moses, biyo bayan tayin sayensa da kungiyoyin Crystal Palace da Everton da Fulham sukayita.
Moses dan Najeriya mai shekaru 27, yana fuskantar kalubalen yawaitar zaman benci bayan zuwan sabon kocin Chelsea Maurizio Sarri, inda zuwa yanzu wasanni 6 kawai ya bugawa kungiyar a karkashin sabon mai horarwar.
Victor Moses wanda ya fi samun karbuwa a zamanin Antonio Conte, ya bugawa Chelsea wasanni 40 a kakar wasa ta 2016/2017 wadda cikinta ta daga kofin gasar firimiya, yayinda a kakar wasa ta bara ya bugawa kungiyar wasanni 38.
A kwanakin baya bayan an kammala gasar cin kofin duniya ya bayyana cewa bazai sake bugawa tawagar ‘yan wasan Najeriya wasa ba saboda yanason ya mayar da hankali da buga wasannin kungiyar da yake wakilta.
Sai dai kociyan tawagar Super Eagles, Gernot Rohr, ya bayyana cewa yana nan yana kokarin shawo kan dan wasan domin yadawo ya bugawa kungiyar wasan cin kofin nahiyar Africa da za’a buga a kakar wasa mai zuwa
A shekarar 2012, Chelsea ta sayi Moses daga kungiyar Wigan kan kudi fam miliyan 9 kuma kungiyar takaishi aro kungiyoyon Liverpool da Birmingham.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!