Connect with us

LABARAI

Majalisar Dattawa Ta Biya Sanata Dariye Alawus Din Naira 85.5 Duk Da Yana Gidan Yari

Published

on

Kusan watanni shida da babbar kotun tarayya dake Abuja ta daure Sanata Joshua Dariye har yanzu yana karbar albashinsa na Naira 750, 000 da kuma alawus na Naira Miliyan 13.5 duk wata daga asusun majalisar kasa, kamar dai yadda jaridar The PUNCH ta ruwaito.
Binciken da jaridar ta PUNCH ta gudabar ya nuna cewa, Dariye, wanda ke wakiltar mazabar Filato ta Tsakiya a Majalisar Dattijai har yanzu yana karbar dukkan alawus-alawsu daga asusun majalisar kasa saboda har yanzu shugabanin majalisar ba su ayyana tallar kujerarsa ba.
Dariye, wanda ya kike mukamin gwamnan jihar Filato daga shekarar 1999 zuwa 2007, ya gurfana ne a gaban mai shari’a Adebukola Banjoko na babbar kotun yankin Abuja bayan da hukumar EFCC ta tuhume shi da allubazarantar da Naira Biliyan 1.162 a zamanin yana gwamna.
A kan haka ne a ka yi masa daurin shekara 14 a gidan yari daga baya kuma kotun daukaka kara da rage zuwa shekara 10 ta kuma tabbatar da daurin a aka yi masa a watan jiya.
Bayani ya kuma nuna cewa, tsohon gwamnan ya kuma yanki takardar takarar kujerar sanata na jam’iyyar APC a kan Naira Miliyan 8, daga baya dai jam’iyyar ta ki amince da bukatar ta sji a watan Satumba.
Da yake tattaunawa da wakilinmu ta wayar tarho, wani hadimin dariye mai suna Mista Christopher John, ya tabbatar da cewa, Dariye da dukkan ma’aikatansa na karbar albashi da alawus alawus daga asusun majalisar tarayya har zuwa yanzu.
Ya ce, Dariye ya daukaka kara zuwa kotun koli, saboda haka ba zama adalci ba iun har aka ayyana kujerarsa a matsayin wanda babu mai shi bayan da bai gama kure sauran hanyoyi na shari’a ba.
John ya kuma kara da cewa, “Ya daukaka karar a saboda haka har yanzu shi ne sanata har sai kotun koli ta yanke hukunci.
“Lallai babu laifin mu ci gaba da karbar albashi tun a har yanzu na a kammaIa shariarba, amwkai wasu sanatoci dake da irin wannan matsalar, kamar Sanata Attah Idoko na jihar Kogi, hukunci ta ba ABM Isaac Alfa kujerar amma tunda Idoko ya daukaka kara, har yanzu yana harkokinsa na majalisa a matsayin sanata har sai an kammala shari’a.
“Dole a ci gaba da biyan hadiman Sanata Dariye albashi saboda har yanzu shi ne ke kan karagar mulki za kua a ci gaba biyansa har sai an kammala shari’a baga daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!