Connect with us

KASUWANCI

NBC Ta Janye Amfani Da Tsaffin Motocin Jigilar Kaya

Published

on

Kamfanin sarra lemon kwalba na Coca-Cola, ya sanar da cewa ya janye yin amfani da tsaffin motocin da yake gudanar da yin jigilar kayan sa da basa iya zurewa yanayi.
Kamfanin ya ce, ya dauki shawawr yin hakan ne domin motocin basa iya jurewa yanayi a bisa daya daga cinkin ka’idojin kamfanin na intanta rayuwar alummar kasar nan.
Magnajan kamfanin a Nijeriya Mista Ekuma Eze, ne ya snar da hakan a hirar sa da manema labarai a garin Fatakwal a ranar juma’ar data gabata, inda ya ce, motocin suna kara janyo dumamar yanayi akan yadda ake yin amfani dasu.
Eze yaci gaba da cewa, baya ga samar da ayyukan yi musamman a tsakain matasa ta hanyar guraben karo karatu da koyar da sana’oin hannu, kuma kamfanin yana tabbatar da yana bayar da gudunmawar sa waje maganje gurbatar yanayi a yankunan da yake gudanar da ayyukan sa.
Ya sanar da cewa, a yanzu motocin dakon mu basa lalacewa akan hanyoyi, domin tuni, mun kwashe su daga hanya saboda basa iya jurewa yanayi.
Acewar sa, “ mun zuba jari da dama a yankunan da muke gudanar da ayyukan mu kuma kamfanin ya rage barin bakin hayaki yana yawo a cikin alumma, inda ya ce, anyi hakan ne ta hanayar kafa na’urar tace guba.”
Akan ingancin kayan da kamfanin yake sarrafawa kuwa Eze ya ce, ana karawa kayan kamfanin inganci a daukacin fadin duniya.
Acewar sa, sanadarin na syrup dake a cikin lemon shi ne ake amfani dashi a daukacin fadin duniya, inda ya ce, a Nijeriya ana yin amfani da gundarin sikari wanda bai kai irin na yadda ake amfani dashi a kasar Amurka ba.
Ya ce, maganar gaskiya itace, ba ko wacce irin Coke bace ake yin amfani da ita ba Nijeriya idan aka yi Magana akan inganci.
Akan masu yi masu na bogi ya yi nuni da cewa wannnan babbar matsala ce da suke fuskanata amma kamfanin yana daukar matakai don dakile hakan.
Ya kuma sanar da cewa, kamfanin ya horas da sama da matasa 13,000 a karkashin shirin sa da ya kikiro dashi don rage zaman kashe wando a tsakanin su.
Acewar sa, “munyi hadaka da gwamnati don tabbatar da an samar da ayyukan yi a tsakain matsana kasar nan, musamman don samar da zaman lafiya a kasar nan.
A nata jawabin Drakta na sashen yada labarai walwalar jama’a na kamafin Sade Morgan ta ce. Kamfanin ya kafa na’urori guda tara a kasar nan, inda ya cena jihar Legas shi ne mafi girma a nahiyar Afirka
A karshe ta ce, kmafanin ya kuma zuba jarin fam biliyan daya daga 2014 zuwa 2023.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!