Sharfaddeen Sidi Umar" />

2019: Buhari Ya Ce Zai Dora Daga Inda Ya Tsaya

Shugaba Muhammadu Buhari a yakin neman zabensa a Sakkwato ya yi alkawalin ci-gaba da kokarin sauke nauyin da al’umma suka dora masa na tabbatar da hadin kan ‘yan Nijeriya tare da tabbatarwa da nasarar kudurorin Gwamnatinsa guda uku.
Da yake yi wa mahalarta jawabi Muhammadu Buhari ya bayyana cewar Gwamnatinsa ta samu nasarar aiwatar da shirin yaki da ta’addanci, tabbatar da tsaron lafiyar al’umma da bunkasa sha’anin tattalin arzikin kasa.
Ya ce “Mun samu nasarar yaki da ta’addanci, shirin mu na bunkasa aikin gona ya habaka kamar kuma yadda muke kokarin shawo kan cin hanci da rashawa. Ina kara tabbatarwa al’umma cewar za mu ci-gaba da wannan kokarin na kare martabar Nijeriya da ‘yan kasa bakidaya.”
Buhari ya kuma godewa al’ummar Jihar Sakkwato kan fitowa da suka yi ba masaka tsinke suka halarci gangamin taron tare kuma da kira gare su da su zabi APC SAK a zaben da ke tafe.
Tun da farko jagoran APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya tabbatarwa al’umma cewar kasar nan za ta ci-gaba da zama a hannun kwarai idan har Muhammadu Buhari ya sake zama Shugaban Kasa a zango ba biyu.
Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su fito ranar zabe su zabi ‘yan takarar jam’iyyar APC da dukkanin ‘yan takarar jam’iyyar domin samun ci-gaba mai amfani da dorewa.
A jawabinsa tun da fari Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Sakkwato Isa Sadik Achida ya tabbatarwa Shugaba Muhammadu Buhari cewar al’ummar Jihar Sakkwato za su fito sosai su zabi ‘yan takarar jam’iyyar PDP a zaben da ke tafe.

Exit mobile version