2019: Sarakunan Gargajiyar Arewa Sun Tattauna Kan Matsalar Tsaro

Sarakunan gargajiya na Jihohin Arewa 19, sub yi babban taron su na yini biyu domin  tattauna wa a kan matsalolin tsaro kafin babban zaben 2019. Bikin bude taron ya sami halartar shugaban hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, da wasu kwamishinonin hukumar, ga mi da shugaban kwamitin Shugaban kasa a kan yaki da shan miyagun kwayoyi, Janar Buba Marwa (ritaya), Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, wanda Kwamishinan kananan hukumomi na Jihar, Farfesa Kabir Mato, ya wakilce shi.

An yi taron ne wanda aka yi masa take da, ‘Perbasibe Insecurity in an Election Year: Prospects and Challenges.’ a Arewa House. Da yake jawabin bude taron, Sarkin Musulmi, kuma shugaban kungiyar Sarakunan ta arewa, Mai Girma, Abubakar Sa’ ad III, ya karfafa bukatar samar da tsaron da ya kamata kafin da lokacin da kuma bayan babban zaben, domin gujewa asarar rayuka da dukiyoyi. Ya bayyana cewa, Sarakuna za su bayar da na su taimakon wajen agazawa jami’an tsaron a lokacin zaben.

A nasa jawabin, shugaban hukumar zaben, ya nanata irin shirin da suka yi ne na tabbatar da zaben ya gudana lami lafiya a bisa gaskiya da adalci. Farfesa Yakubu, ya shaida wa manema labarai jim kadan bayan tashi daga taron cewa, wasu ‘yan siyasan na kasar nan sun faye son kansu. “Wasu ‘yan siyasar namu ba ma’abota Dimokuradiyya ne ba, shi ya sanya yau ka gan su a wannan Jam’iyyar, gobe kuma sun tsallaka sun koma waccan,” in ji shi.

A ganawar da ya yi da manema labarai jim kadan da gama tattaunawar na su da Sarakunan, Shugaban kwamitin Shugaban kasa a kan yaki da shan miyagun kwayoyi, Janar Buba Marwa (ritaya), ya yi wa manema labarai karin haske ne a kan tattaunawar na su, inda yake cewa, “Na nemi goyon bayansu ne, saboda Sarakuna suna da karfin gaske a arewa, ana sauraronsu, da su taimaka mu hada hannu wajen magance wannan muguwar dabi’ar da ke yi mana illa a kullum. Na kuma kawo maganan almajirai, inda na nuna masu cewa, ba wai almajirancin ba shi da kyau ne ba, amma akwai gyaran da sashen na almajiranci yake bukata a halin yanzun, domin kana iya ganin yara ko ta ina, suna shaye-shaye, wadanda kuma almajiran ne, ba karatu suke yi ba.

Wannan aiki ne na musamman wanda aka dora mana, wanda kuma nan da watanni kadan, uku ko hudu, za mu kammala mu kuma mika rahotonmu. Maganan shaye-shaye, magana ce babba, wanda ba wai masu shaye-shayen ne kadai za ka tunkara ba, farko ma kamata ya yi ka toshe hanyoyin da ake samun abubuwan da ake sha din, saboda matukar babu ababen da ake shan, to ba za ka samu masu sha ba. Don haka, za mu bi duk inda kwayoyin ke fitowa, daga tushen su har kasashen waje mu tabbatar da duk mun toshe su. Misali ta inda ake shigo mana da su nan cikin kasarmu, kamar wannan kwayar da ake kira Tramadol, a yanzun haka, an kama Tramadol kwantaina sun kai 100, a tashoshin Jiragen ruwa. Sama fa da kwali dubu sau dubu kenan, bilyan!

 

Exit mobile version