An share kusan makwanni biyu ana ta faman zabukan fidda gwani a cikin jam’iyyun kasarnan. Su wadannan ‘yan takara ne za su wakilci jam’iyyun da suka tsayar da su a zaben kasa da za a gabatar shekara mai zuwa ta 2019. Hukumar Zabe ta Kasa ta shata iya kwanakin da ya dole kowacce jam’iyya ta fitar da gwanin da zai mata takara. Amma dai abubuwan sun zo da korafe korafe.
Jam’iyyar APC mai mulki wanda a ka kafa ta bisa cewa za ta tabbatar da adalci a kasa da kuma ganin an samar da dimokaradiyyar cikin gida a cikinta ta da fifita bukatun jama’a da mutunta abin da suke so suka kuma zaba. Shakka babu wannan manufa ta samu tangarda ainun a wadannan zabukan tsai da gwani da a ka gabatar. Mai yiwuwa shekara hudu kenan da binne wannan manufa ko kuma manufar tana aiki ne lokacin da jam’iyyar ba ta kan mulki, amma yanzu tun da kidan ya canza rawar ma sai ta canza.
A wannan zabukan wasu kiri-kiri an kwace musu kujerunsu ba domin sun saba da manufofin ita jam’iyyar ba, sai domin ko dai basa biyawa wasu daga cikin jigogin jam’iyyar bukatunsu, ko kuma sun samu matsala da gwamnonin jihohinsu duk da fa an zabe su ne ba domin biyawa wani bukatarsa ba sai domin su yi wa al’ummarsu wakilci nagari.
Abubuwan da suka faru ba zai zama da matsalar da zata baiwa mutane mamaki ba idan da misali a ce a babban jam’iyyar adawa ta PDP ce. To amma a jam’iyyar da ta yi ikirarin kawo gyara a dimokaradiyya da kuma canza fasalin tafiyar siyasar Nijeriya, lallai akwai damuwa sosai a irin wannan salon karfa karfa na fito da ‘yan takararta. Wato a takaice dai, kakabawa mutane ‘yan takara a siyasar kasar nan za a iya cewa ba a rabu da Bukar ba an haifi Habu.
Da bukatar jagororin jam’iyyar ta APC su saurari korafe-korafen wasu daga cikin ‘yan takarar da irin yadda a ka yi musu magudi. Ko ba komai daga cikin abubuwan da suka haifar da faduwar jam’iyyar PDP akwai kama karyar cikin gida. Na kalli wasu daga cikin zabukan fitar da gwanin, wasu kuma ji nayi to amma lalle akwai bukatar a tuna cewa ita fa dimokaradiyya gwamnati ce ta jama’a kuma domin jama’ar.
Cikin wadanda suka koka akwai ita kanta matar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta kira zaben fidda a gwanin da rashin adalci a jam’iyyar ta APC ta kuma yi Allah wadai da shugabancin jam’iyyar. Tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda Sulaiman Abba wanda yanzu ya tsunduma fagen siyasar tsundum, ya kuma nemi tsayawa takarar sanata na Jigawa ta tsakiya a can jiharsu ta Jigawa. Shi ma ya koka da rashin adalcin da aka tafka masa na murdiya,shi ko sunansa ma babu a jerin ‘yan takarar duk da cewa ya cika dukkan ka’idar da aka shimfida.
A jihar Zamfara ki-ki ka-kar da ta faru ban san ko irinta ta taba faruwa a tarihin dimokaradiyyar Nijeriya ba. In da za a ce jam’iyya ta ta shi fam fam fam babu dan takara. Saboda kasa samun daidatuwa a zaben fitar da gwanin har ranar da a ka iyakance za a karbi sunayen ‘yan takarar ta cika. Ba kuwa a nan dambarwar ta tsaya ba, an yi doki-in-doka tsakanin mutanen da ko a bariki ya kamata suyi tunanin su fa yanzu dattijai ne masu koyawa na baya yadda za su tafiyar da rayuwarsu a gaba. A wani gajeren faifan bidiyon da na gani tsakanin mai goyon bayan gwamna Abdul Aziz Yari da kuma da alama mai ja da shi abin kaico ana rirrike Sanata Kabiru Marafa shi da Ikra Bilbis suna baiwa hammta iska kamar damben Shago da Dan dunawa.
A jihar Kaduna jikakkiya ce tsakanin Sanata Shehu Sani da gwamnan jihar Nasiru Elrufa’i. Da ma dai duk mai bibiyar turnukun siyasar ta Kaduna a wannan ‘yan watanni ya san za a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Domin tun lokacin da Sanatocin suka ki goyon bayan bukatar gwamnan jihar a kan su lamunce masa ya ciwo bashi a kasar waje dangantakar tasu ta kara tsami sosai.
Idan ma dai akwai wata to wannan din dai ce ta fi fito da rigimar ta su a fili, saboda kamar wasan yara sai ga gwamna ya manta da girman kujerar da yake hawa ya fito bainar jama’a yana ruwan tsinuwa ga sanatocin da su ka shure wañnan bukatar ta sa ta ciwo bashin wato Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi!
Shi Sanata Suleiman Hunkuyi har gidansa mai rusau ya rusa, da yaga bashi da wuri a jam’iyyar ta APC din Kadunan tuni sai ya canza sheka zuwa jam’iyyar PDP. Amma shi Sanata Shehu Sani ya zauna a jam’iyyar kuma har ya yanki takardar neman komawa takarar kujerar sanatan. A halin da ake ciki yanzu ita uwar jam’iyya ta kasa ta amince da Sanata Shehu Sani ci gaba da takarar sanata a zabe mai zuwa. Shi kuma gwamna ya yi wurgi da wannan matsaya ta uwar jam’iyya bilhasali ma ya kaddamar da zaben cikin gida ya sa an zabi Uba Sani a matsayin dan takarar kujerar sanatan na Kaduna ta tsakiya.
Wutar rikicin ta na ta ci, na saurari wani faifan murya da shi sanata Shehu Sani yake jaddada matsayinsa na babu mutumin da ya isa ko domin shi gwamna ne ya hana shi fadin albarkacin bakinsa,ko kuma ya tursasashi yin abin da a fahimtarsa bai cancanta ya yi ba. Dangane da wannan dambarwa ta kai matsayin da har shugaban jam’iyyar ta kasa Adams Oshomhole ya jaddada cewa Shehu Sani ne dan takararsu sannan idan Elrufa’i ba a shirye yake ya bi tsarinsu ba to ya koma tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP.
A jihar Ikko shi kuma gwamnan mai ci ne aka kwace takarar aka baiwa wani. Laifin Ambode an ce ba wai domin ya ki yiwa mutanen Ikko wani abu bane. Matsalarsa ce da uban jam’iyyar APC ta kasa wato Bola Ahmed Tinubu. Da alama shi Bola yana so ya juya gwamnan yadda ya ke so saboda tun da shi ne ya yi shi, shi kuma gwamnan ya nu na a batun mulki ba a sarki da wan sarki hakan ne ya sa Bola Tunibun ya nu na masa ta yaro kyau take bata karko.
Ita kuwa kujerar uban tafiyar cewa aka yi babu mai ja da shi. Shi kadai ya fito babu hamayya. Wannan ita ce dimokaradiyya samfurin Nijeriya. Dole ko dai a bi liman sallah ko kuma a canza masallaci.
Sai dai duk a wannan abubuwan abin da kowa ya damu shine yadda za ta kaya a zaben 2019 musamman na shugaban kasa. Ganin ‘yan takarar da za su gwabza da kuma turnukun da zai kaure tsakanin shugaba mai ci Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC da kuma Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.
Ga Alhaji Atiku Abubakar da ma ce daya dade yana nemanta amma bai samu ba sai yanzu wato samun tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta PDP sau biyu yana ficewa daga jam’iyyar saboda rashin tsayar da shi takarar. Akwai siffa guda da ta hada shugaban kasa Muhammadu Buhari da Alhaji Atiku Abubakar siffar ba ta wuce damuwa da mulkin Nijeriya ba. Yanzu shugaba Buhari ya samu ya dandani dadin kwanan Dutsen Aso wanda da wuya ya iya yarda wannan damar da kubuce masa. Domin samun wannan kujerar kuwa, Atiku Abubakar a shirye yake ya batar da duk abin da zai iya bayarwa saboda samunta.
Musamman a yanzu da tsammanin da su ka yiwa gwamnatin ta Buhari ta ba su mamaki. An musu alkawura fiye da sau shurin masaki,amma duk abin ya zama gafara sa ba a ga kaho ba. Shekaru uku zuwa hudun na Buhari ya fito da abubuwan da ba domin ya samu mulkin ba babu yadda hankali zai yarda da cewa kusa da hakan zai iya faruwa.
Duk wani fata da talakan da ya zabi gwamnatin nan ya yi bai samu wannan abin ba. Wani abu ma sai dai kishiyar hakan ake ta gani. Ina alkawarin sauko da farashin mai? Maimakon haka cire tallafi a ka yi dungurun uwar du. Ina alkawarin tallafin kudi ga masu karamin karfi? Hatta jihohin da a ka ce an fara bayarwa su ma ya zama labari. Ina maganar tsaro? A Zamfara har gwamnan jihar ya taba cewa a daina kiransa da shugaban tsaro na jiharsa.Ko ma dai menene zaben 2019 turnuku ne tsakanin giwaye biyu.