Connect with us

BIDIYO

Fittaccen Jarimin Bollywood Kader Khan Ya Rasu

Published

on

Fitattaccen jarumin fina-finan Bollywood na kasar Indiya, Kader Khan, ya rasu yana da shekara 81 a duniya, rahotanni daga kasar Indiya sun ce ya rasu ne a wani asibiti a kasar Kanada bayan ya dade yana fama da wata cutar da ta shafi kwakwalwa. Za ayi jana’izar Khan ne a kasar Kanada inda iyalansa suke kamar yadda dansa Sarfaraz ya shaidawa kafafen watsa labarai a Indiya. Khan ya rasu ya bar ‘ya’ya biyu da mata guda daya.

Kader Khan wanda musulmi ne ya fito a fina-finai sama da 300 na Bollywood a tsawon rayuwarsa. Tun a 1973 ya fara fim inda ya fito a wani fim mai taken ‘Daag’ tare da shi da Rajesh Khanna da Sharmila Tagore. Yana fitowa a matsayin bos da kuma uba kafin ya koma yana wasan barkwanci a wajajen 1990.

Kader Khan ya dade yana rubuta labarin fina-finai kafin ya fara fitowa a fim.Ya rubuta labarin fina-finai da dama da suka yi fice, kamar ‘Coolie’ da ‘Amar Akbar’ da ‘Naseeb’ da ‘Aankhen.’ ‘Mukaddar Ka Sikandar.’

An haifi Kader Khan a  birnin Kabul dake kasar Afghanistan, amma daga bisani iyayensa suka koma Mumbai dake kasar Indiya. Mahaifinsa dan asalin Afganistan ne yayin da mahaifiyarsa ‘yar kasar India ce.

Abokan aikinsa a harakar fina-finansa da dama ne suka bayyana alhinin rashin Kader Khan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!