Connect with us

TATTAUNAWA

Albarka Multi Purpose Ta Zama Abar Koyi Ga Sauran Kungiyoyi A Funtuwa —Hajiya Halima

Published

on

Wakilinmu BALARABE ABDULLAHI ya sami dammar tattauna wa da shugabar kungiyar Albarka Multi Purpose Co-Operayibe Society da ke garin Funtuwa ta jihar Katsina HAJIYA HALIMA IDRIS. Da farko ta bayyana yadda suka fara wannan kungiya da ayyukan da suke yi da nasarorin da suka samu da kuma matsalolin da suke fuskanta a yau.

Ga dai yadda tattaunawar shugabar ya kasance da wakilinnamu:

Yaushe ku ka kafa wannan kungiya ?

Mun kafa wannan kungiya shekara bakwai da suka gabata, mun fara a tsakaninmu ba mu wuce mu biyar ba, amma daga baya, sai aka ba mu shawarar ya kamata mu fadada wannan kungiya, wato mu gayyato mata da suke da tunanin tafiya a wannan kungiya.

Amma a lokacin da muka gayyaci wasu mata sai muka yi wa kungiyar rijista, amma kafin yin rijistar, mun yi shekara da yawa, mu na tallafa wa junanmu, da mu ka yi tunanin kafa wannan kungiya tare da gayyatar wasu mambobi, sai mu ka yi wa wannan kungiya rijista, shi ne a yau zan iya cewar, muna da shekara bakwai da fitowarmu fili kowa ya sanmu.

 

Ta wasu hanyoyi ku ke bi, ku ke tallafa wa junanku, daga kafa wannan kungiya zuwa wannan sabuwar shekara ta 2019?

Tun farko mu na tallafa wa junanmu, a lokacin da muka ga lokacin da daya daga cikinmu za ta aurar da ‘yar ta,abubuwanda muke yi ma ta kyauta su ne kamar toye-toye abinci da kayayyakin kicin da, a wasu lokaci kuma, sai mu yi wa wasu ajon kudi mai yawa, mu ba su, a matsayin tallafi, ba bashi daga kungiyarmu ba, domin duk wadda aka ba ta, babu maganar ta dawo da abin da aka ba ta.

Kuma wani abin sha’awa shi ne mu da kanmu muke zama mu tattauna yawan kudin da za mu ba ‘yar kungiyarmu tallafi, in mun samu matsaya na yawan kudin da za a ba ‘yar kungiyar da za ta aurar da ‘yar ta, sai mu kasa wannan kudi a tsakaninmu, ba tare da bata lokaci ba, sai mu hada, a cikin lokaci kuma, mu ba ‘yar kungiyarmu, a matsayin gudnmuwa.

 

In aka tallafa wa ‘yar kungiya, sai wani sha’anin ‘yar kungiya ya tashi, sai wadda aka tallafa ma ta, bat a da kudin da za ta bayar a matsayin na ta gudummowar, wane mataki ake dauka ga wadda ba ta bayar da na ta gudummowar ba ?

Babu komi, domin duk dan adam, ya san babu, babu wani mataki da muke dauka ga wadda ba ta sami damar bad a na ta tallafin ba, wane ne ya sa, a tsarinmu, in mun lura wasu daga cikinmu, ba su da jarin yin wasu sana’o’i,mu kan hada kudade ma su nauyi, mu ba ‘yan kungiyar da suke bukatar jari, kuma in mun ba su, za mu umurce su da su rika dawo da tallafin a lokacin da suka ga ya dace, amma mu kan ba duk wadda mu ka ba tallafin jarin shawarar irin sana’ar da za ta yi da kudin da za mu ba ta.

 

Daga fara bayar da wannan tallafi, za ki iya tuna ‘yan kungiya suka sami wannan tallafi daga shugabancin da mu ke yi?

A gaskiya, farar da gareje, in bayyana ma ka yawan wadanda muka tallafa ma su, da kamar wuya, domin wasu a dalilin aure ko kuma canjiin aiki na mazajensu, sun canza gari, wasu kuma Allag ya karbi rayuwarsu, a gakiya abin da zan ce ma ka shi ne, wadanda suka sami tallafin jari a wannan kungiya ta mu, suna da kwarai da gaske. Sai dai a kusa-kusan nan akwai mata fiye da goma da suka sami wannan tallafi, kuma sun sami canijn rayuwa a dalilin shigarsu wannan kungiya ta mu.

 

A tsakanin gwamnati da kuma ‘yan siyasa, a ina ku ka taba samun wani ko kuma wasu tallafi domin ci gaban wannan kungiya?

A gaskiya tun da mu ka kafa wannan kungiya, har zuwa lokacin da mu ka yi ma su rijista, ba mu taba samun wani tallafi, daga wuraren da ka bayyan ba,musamman ‘yam siyasa, sun sha yi mi ni alkawari ba mu tallafi, amma, ko da dan siyasa daya a karamar hukumar Fuuntuwa, bai ba mu wani tallafi ba.

Zan iya tuna wa, suka ziyarce mu, a ce za a ba mu rancen kudi, ko tallafi ko kuma rance, mu yi noma ko kiwo, an dai ma na mai a baki, amma har zuwa wannan rana, ba mu shaida ba daga gwamnati ko kuma wani dan siyasa.

Sai dai b azan manta ba, karamar hukumar Funtuwa ta hada mu da wata kungiya mai suna RUFIN, wadda ba rance suke bayarwa ba,sai dai ta ba ka shawarar yadda kungiya za ta sami kudi, ta koya maka yadda za ka yi kasuwandci da kudin da ka samu daga shawarwarin da suka ba ka, har takardar shaida sun ba mu na yadda za mu rika yin adashi a tsakanimu. Zuwa yanzu mu na aje wadannan kudade a banki, sai karshen shekara muke dauko su mu rarraba a tsakanimu, domin duk dan kungiyarmu, yana da sana’a a yau, shi ya sa muke juya wa wannan kudi baya.

 

Kin ce ba wani dan siyasa da ke ba ku tallafi, ga shi za a yi zabuka a wannan shekara, ba za ku yi zabe ba ken an?

Babu ko shakka, za mu yi zabe, sai dai kuma mun yanke shawarar yin zaben ne, domin mu sauke nauyin da tsarin mulkin Nijeriya ya dora ma na, na mu zabi wanda ya dace, juya ma na baya da suka yi, bai sa mu ki yin zabe ba.

 

Akwai wasu sabbin tsare-tsare da za ku aiwatar a wannan sabuwar shekara ta 2019, domin ci gaban mambobin wannan kungiya ta ku?

Lallai muna da tsare-tsaren da za mu aiwatar a wannan sabuwar shekara, musamman dai za mu fi mayar da hankali wajen kara samun mata a wannan kungiya da za mu koya ma su sana’o’in dogaro da kai da  kara bunkasa tallafin jari ga mambobinmu da kuma kara tashi na ba su shawarwarin da za su tallafa wa wasu matan da ba su da sana’o’in da za su dogara da kansu, abin da muka sani shi ne, saboda mayar da hankali da muka sa a gaba,na tallafa wa kanmu, ba tare da waiga wa baya ba, Albarka ta zama abar koyi ga sauran kungiyoyi da karamar hukumar Funtuwa da kuma jihar Katsina baki daya.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!