Connect with us

TATTAUNAWA

Sarki Sanusi II Ya Bar Jaki Ya Na Dukan Taki – Sani Brothers

Published

on

A cikin tattaunawar fitaccen dan kasuwar nan kuma dattijo a yankin Arewa ta Najeriya, ALHAJI SANI BROTHERS, ya ke yi da Editan LEADERSHIP A YAU LAHADi, NASIR S. GWANGWAZO, duk mako, a wancan satin sun tsaya ne inda dattijon ya ke cigaba da batu kan tattalin arzikin kasa da yada za a dakile cin hanci da rashawa. A wannan makon Baba Sani Brothers ya dora ne kan fahimtarsa kan batun badakalar canjin kudi, sannan ya gangaro da ra’ayinsa kan matsayin da masana tattalin arziki irinsu Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II su ka dauka kan batun rage tallafin mai a lokacin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma a yanzu da shugaban kasa mai ci Muhammadu Buhari a ka ce ya janye shi dungurugum. Ga yadda hirar tasu dai ta cigaba:

Ka yi bayanin cewa, a na bayar da mabambantan kudin canji a Najeriya. Shin ka na da misalin irin wadanda a ke bai wa ne?

To, ka san duk abinda dan Najeriya ya yi, idan alkali ba za ka ce da shi barawo ba. Shi ya sa za ka ji an ce mutum ya saci biliyoyin Naira sai a tafi kotu a yi ta shari’a, a ce ai zargi a ke yi har sai alkali ya tabbatar ma sa da laifinsa, sannan ya zama mai laifi. Amma Ina da kyakkyawan bayani cewa, akwai wadanda su ka zo su ke so za su kawo ‘AGO’…

 

Mene ne ‘AGO’?

Man da babbar mota ta ke amfani da shi. Shi kuma wannan mai da babbar mota ta ke amfani da shi, an yi ‘deregularting’ dinsa tun lokacin Obasanjo, amma saboda abinda mu ke fada na ‘corruption’ da cin hanci na NNPC, an ki yarda a wadata shi yadda kowa zai wadata. Saboda haka wadannan abokan harkar tasu su ke kawo shi da kadan-kadan. Su irin wadannan su ne a ke cewa a na ba su a kan Dala daya a Naira 305. Amma idan ka ba su a kan Naira 305 din, idan sun ce su na so za su kawo ma ka lita miliyan 10, sai su je su kawo ma ka lita miliyan biyar. Shi wannan miliyan biyar din a yanzu Ina tabbatar ma ka da cewa su na sayar da shi a Naira 260. Saboda haka idan ka bada ‘subsidy’, ai ‘subsidy’ din bai je kan talaka ba tunda wannan gas din da shi za a zuba wa babbar mota ta dauko kowanne irin kaya. Kai hatta jirgin kasa su dauko kowanne irin kaya tun daga Lagos su kai kowanne bangare na arewacin Najeriya. To, tun da sun tsauwala ma na, ina ka ke jin za ka samu saukin dako? To, saboda haka meye amfanin ‘subsidy’ din da a ka ba su? Ka ga ‘sunsidy’ din da a ka ba su baida amfani.

 

To, da ma tun kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki a lokacin da man fetur ya ke Naira 87 kafin ya hau ya cire tallafin man ya koma Naira 145, akwai masu cewa da ma tallafin man sata ce. Mene ne ra’ayinka kan hakan?

Gaskiya ai na yi ma ka misalai a baya, na ce da kai akwai wadanda su batagari ne. mutum zai zo ya kawo mai lita miliyan biyar, amma kuma a takarda ya ce miliyan 10 ya kawo, a ba shi tallafi a matsayin miliyan 10. Ka ga wannan zalunci ne. Ina fata ka gane. Kuma gabadaya yanzun su wancan kudi da ’yan kasuwa su ke cewa su na bin gwamnati Naira biliyan 800, bashin da ne na wancan gwamnatin tunda wannan gwamnatin an ce an cire tallafin mai? Ni tambayata ma kenan.

 

Idan na waccan gwamnatin ne, ba sai wannan ta dora ba tunda shi mulki ai cigaba ne?

Akwai mulki cigaba, amma ni a ra’ayina… Zan iya tunawa akwai wani lamari da a ka taba samu cewa, an lalata Bank of the North (Bankin Arewa), sai a ka ce a na neman shawararmu, mu ‘yan kasuwa, cewa yaya za a yi da shi? Sai na ce, to an ce gwamnoni sun ranci kudi… Da su ka ranci kudi sai su ka yi wasu abubuwa da su yi wasu abubuwa wadanda kudi ba su dawo ba… Sai na ce idan an duba takardu masu kyau na gaskiya, idan gwamna aiki ya yi da shi, to kudin nan ya na kan gwamnan da ya gaji shi da ya biya. Idan kuma ya diba ya yi bukatarsa ta kashin kansa, to sai a nemo shi ya zo ya biya. Saboda haka idan an bincika an tabbatar da gaskiyar cewa mutanen nan su na bin bashi, ba harabe babu zalunci babu hadin baki, to sai a biya su. Amma idan an gano akwai makirci, sai a kai mutum gaban shari’a ya fadi ya a ka yi. Ka ga ba a ci hakkin kowa ba, ba a kuma ci hakkin mutanen kasa ba. To, ni ra’ayina kenan.

 

To, amma ba ka ba mu cikakkiyar amsa a kan shi tallafin mai da a ka ce a na bayarwa ba, inda ko da a baya kamar Sarkin Kano, wanda kwararre ne a kan tattalin arziki, ya taba fadar cewa ‘subsidy’ da gwamnati ta ke bayarwa a wancan lokacin na tsohon shugaban kasa Jonathan, zalunci ne kuma yakamata a cire shi, gara a matsawa gwamnati ta rika yin abinda yakamata da kudin, ba a rika bada tallafin mai ba kuma lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya zo sai ma ya cire shi gabadaya. Shin meye ra’ayinka?

Kullum wadanda su ke kiran kansu ‘economist’, ni gabadaya ma ban yarda da su ba! Kamar yanzu ka ce Sarkin Kano ya yi gwamnan Babban Banki… na san wannan, ka ce ‘economy’ ya san tattali, amma kuma ya kasa rike fadarsa, domin ya samu kudi ya lalata. Har shari’a a ka kai shi… Ah! Ba maganar gaskiya ba ce? Shi me ya sa ya yi wannan? Ai kullum ba zai zama ka take laifinka ka hangi na wani ba! Ina fata ka gane. Duk mutumin da a ka ce har an buga a jaridu, har an tafi majalisa, daga baya an zo an kama kafa an bar zancen ya shige. Ka ga idan akwai irin ma, ai babu yadda za a hana cin hanci da rashawa. Shi can da ya ke nema a hana ‘corruption’ me ya kawo a fadarsa irin wannan zance? Kuma a ka je a ka samu manya su ka zo su ka hana abin. Ka ga kenan ashe shi ‘corruption’ din naka ka ke takawa ka hangi na wani.

 

Za mu cigaba a makon gobe in sha Allah.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!