Connect with us

ADABI

Sharhin Littafin ‘Zuciyarka Jagorarka’ Na Mustapha Ibrahim Abdullahi

Published

on

Littafi:  Zuciyarka Jagorarka

Marubuci:  Mustapha Ibrahim Abdullahi

Manazarci:  Adamu Yusuf Indabo

Madaba’a:  IGM Publishers

Shekarar Bugu:  2018

Yawan Shafuka:  32

Farashin Littafi:   N150

Lambar Isbn:  __ __ __

 

Mustapha Ibrahim Abdullahi matashin marubuci ne, wanda ya yi fice a wajen rubuta rubutattun wakokin turanci da kuma rubuce-rubucen kimiyya, da rubutun sanya wa mutane karsashi da azama a al’amuransu (Motibational Books). Ya shigo duniyar rubutu tun a shekara ta Dubu Biyu Da Sha Hudu (2014). Memba ne na kungiyar marubuta ta kasa reshen jahar Kano (ANA KANO) da kuma kungiyar masu rubutun kirkira ta jami’ar Bayero wato ‘Creatibe Writers’ Forum Bayero Unibersity Kano’. Ya rubuta littattafai da dama da suka hada da: Ka San Jikinka, Illar Taba, Rayuwar Dan Adam, Rumbun Hikima, da kuma Zuciyarka Jagorarka wanda shi ne littafinsa na farko da ya fara wallafawa.

Littafin mai suna Zuciyarka Jagorarka na yin bayani ne kan tsokar halittar nan dake cikin farfajiyar kirjin ababan halitta wacce ke aikin harba jini zuwa sassan jikinsu wato zuciya. Ita dai zuciya ana samun ta ne a jikin rukunin halittar da jini ke gudana a jikinsu dangin mutane, dabbobi, tsuntsaye, kadangaru, da ma duk halittar da jini yake gudana a jikinta.

Marubucin littafin ya fara ne da kawo Hadisin fiyayyen halitta (S.A.W.) da yake cewa: “A cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru. Idan ta baci dukkan jiki ya baci. Fadaku ka ji ita ce zuciya.” Daga nan kuma ya gangara da bayaninsa inda yake sanar da makaranta ko mece ce zuciya, da bigiren da take zaune a cikin kirazan abun halitta, da abubuwan da ta kebanta da su, da ayyukanta, da lokacin aikinta da na hutawa, da kuma lafiyarta, da yadda ma’abocinta zai ba ta rigakafin kamuwa da cutukan da suke illatar da ita. Marubucin ya fada mana cewa ita ce gabar farko da take fara yin aiki a jikin mutum tun yana cikin mahaifa dan sati Uku, kuma dai ita ce ta karshen daina aiki idan rayuwar mutum ta kare, domin zuciya ita ce gabar da koyaushe cikin aiki take ba dare ba rana, ko mutum yana cikin yanayin aiki, ko hutawa ko kuma bacci, ita aikinta kawai ta ke kaddamarwa. Zuciya ke nan, wacce kaf kafatanin jikin mutum ita ce gabar da take kaddamar da aikinta ba tare da karbar umarni daga kwakwalwa ba.

 

Zubi

Marubucin littafin ya kasafta littafin ne izuwa babuka Goma, wanda hakan ya matukar saukakawa mai karatu. Sannan ya yi amfani da sassaukar Hausa kuma karbabbiya. Sannan ya yi kokari matuka wajen kiyaye ka’idoji da kuma alamomin rubutu. Sai dai ‘yan kurakuran da ba a rasa ba saboda ajizanci da ba ni adam yake da shi.

 

Darussa

– Babban darasin da mutum zai dauka daga littafin na ‘Zuciyarka Jagorarka’ shi ne sallamawa da ganin girman Allah  subhanahu wata’ala, wato Injiniyan injiniyoyin da ya halicci dukkan injiniyoyi kuma ya kera zuciya. Lallai Allah Wandara shi ne Gwani Mai tsara halitta ba tare da samfur ba.

– Koyar da hanyoyin kula da lafiyar zuciya da suka hada da cima mai kyau wacce ba lafiyar zuciya kadai ke karawa ba har ma da lafiyar jiki gaba daya. Motsa jiki domin yana karfafa lafiyar zuciya ta hanyar gina tsokar zuciya, kuma ya kone kitsen dake taruwa a hanyoyin jini, sannan ya rage cutar nan ta hauhawan jini. Kawar da damuwa saboda damuwa illa ce ga lafiyar zuciya da kwakwalwa da ma lafiyar jiki gaba daya.

– Sanin hakikanin tsokar zuciyar zahirinta da badininta.

– Kuma littafin zai taimaka wa daliban kimiyya kara fahimtar karatunsu musamman masu karantar likitanci da kuma masu nazarin halittar dan adam.

 

Abin Burgewa

Littafin ya samu kyan bugu, kama daga bango zuwa takardar ciki. Saboda an yi amfani da bango mai kyau da yake mai santsi da kuna daukar idanu. Haka takardar ciki ma an yi amfani da kyakkyawar farar takarda ba dususu ba. Sannan rubutun ya fita tar kuma balo-balo, yadda ko masu raunin idanu za su iya karantawa ba tare da sun yi amfani da gilashin kara gani ba.

 

Kurakurai Da Shawarwari

-Rashin lambar ISBN nakasu ne mai girma ga littafin ilimin kimiyya kamar ‘Zuciyarka Jagorarka’, saboda littafi ne da dalibai za su iya yin amfani da shi, ba wai na kasuwar adabi ne ba.

– Ya kamata a ce an yi amfani da hotuna da suke nuna kowacce gaba ta zuciya a lokacin da ake magana a kan ta, amma sai hakan bai samu ba.

– Bisa la’akari da tasirin addini ga marubucin, wanda ya bude littafin ne ma da Hadisin fiyayyan halitta, to ya kamata a kawo hanyoyin tsarkake zuciya. Da yadda za a samar mata da nutsuwa da kuma yadda za a wanke zuciya daga mummuna zuwa kyakkyawa da addini ya tanada.

To a karshe dai dole ne a jinjinawa Malam Mustapha bisa wannan namijin kokarin samar da wannan littafi mai suna Zuciyarka Jagorarka. Saboda littafi ne da babu irinsa kuma ake da bukatar ire-irensa cikin harshen Hausa, musamman ma don taimakawa dalibai da suke da sha’awar karanta kimiyya. Fatan Allah ya kara hasken makaranta, kuma ya sa littafi na biyu ya zo da abubuwan da littafi na daya ya rasa Ameen.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!