Connect with us

KASUWANCI

Manoman Shinkafa 12,000 Za Su Amfana Da Shirin Lamuni Na Bankin CBN A Jihar Kano

Published

on

Akalla manoman Shinkafa dubu 120, 000 a jihar Kano za su amfana da shirin gwamnatin tarayya na ba da bashi ga w3adanda za su yi noman rani. Alhaji Abubakar Aliyu  Shugaban kungiyar manoman Shinkafa ta Nijeriya wato RIFAN reshen jihar Kano shi ne ya bayyanawa Kamfanin dillancin labaran Nijeriya hakan a wata tattaunawa da suka yi da shi a jihar Kano a yau Talata. Ya ci gaba da cewa; sunayen Manoman da suka yi Rijista tuni aka turawa babban Bankin Nijeriya wato CBN domin tantancewa don ba su wannan bashin. Ya tabbatar da cewa; akalla kowanne Manomin Shinkafa za a bashi Bashin da bai gaza Naira Dubu 220 domin ya samu ya biya kudaden da za a rika yi masa ayyukan noman.

Ya tabbatar da cewa; akalla manoma dubu 150 ne suka yi rijista da shirin, amma adadin ya ragu ne zuwa dubu 120 sakamakon matsalar BVN da aka samu. Ya ce; tuni aka aikawa Babban Bankin Nijeriya wato CBN sunayen domin tantancewa don ba da wadannan kudade da gaggawa, domin kuwa a kwanan nan za a fara noman ranin. Sai dai ya baiwa wadanda suka samu matsala da BVN hakuri, inda ya ce; za a tabbata a yayin ba da basussuka a lokacin noman damina an ba su. Sannan ya shawarci wadanda suka yi nasara har aka zabe su aka tura sunayensu da su yi amfani da wadannan basussuka da za a ba su wajen bunkasa noman shinkafa a jihar da ma kasarnan baki daya. Ya jaddada cewa; yin noman Shinkafa ne kawai a kasarnan zai ba da damar daina shigo Shinkafa daga kasashen ketare.

Rahotanni sun nuna cewa; akalla Hekta dubu 5 ne ruwan sama ya lalata na noman Shinkafa a kananan hukumomi 10 na jihar Kano a cikin shekarar 2018, wanda manoman dake karkashin wannan shirin ne abin ya shafa, inda aka kiyasta cewa; sun yi asarar akalla Naira Biliyan 5 sakamakon lalata Shinkafar da ruwan saman ya yi a jihar.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!