Connect with us

TATTAUNAWA

Mun Samu Nasarori A Jihar Kaduna A Shekara Ta 2018 -Mai Izala

Published

on

Wakilinmu da ke Zariya, BALARABE ABDULLAHI ya samu damar zantawa da babban jami’in tsare –tsare na hukumar kula da tsaro ta jihar Kaduna, (Kaduna State Bigilance Serbices), shugaban jami’an hukumar a kananan hukumomin jihar Kaduna 23, kuma shugaban wannan hukuma a karamar hukumar Sabon Gari, ALHAJI LAWAL AHMED, wanda aka fi sani da Mai Izala, inda da farko ya bayyana wa wakilinmu wasu nasarori da wannan hukuma ta samu a karamar hukumar Sabon Gari da kuma jihar Kaduna baki daya. Ga yadda tattaunawarsa ta wakilinnamu da ke Zariya.

Wasu nasarori ku ka samu a wannan hukuma a jihar Kaduna?
Kamar yadda wasu al’umma da yawa suka sani a jihar Kaduna, kafin fito da wannan hukuma, a kwai matsalolin tsaro ma su yawan gaske a daukacin jihar Kaduna, a lokacin da mai girma gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’I ya lura da matsalolin tsaro da ya gada, sai ya kafa wannan hukuma, da nufin kawo karshen wadannan matsaloli na tsaro a fadin jihar Kaduna.
A gaskiya, idan na ce zan bayyana nasarorin da mu ka samu, za mu kwashe sa’o’I ma su yawan gaske, ban kammala ma ka bayanin nasarorin ba. Mun fara wannan aiki a kalla shekara biyu da suka gabata, bayan mai girma gwamnan jihar Kaduna ya kaddamar da mu, a matsayin hukuma ta samar da tsaro na sa kai a fadin jihar Kaduna.
Na farko, duk wanda ke jihar Kaduna, musamman a garin Kaduna, ya san batun wasu gun–gun–gun ‘yan ta’adda da ake kiransu ‘Yan Shara,bayan ya kaddamar da wannan hukuma, sai mu ka fara karya kumallo da wannan ‘yan shara da na bayyana ma ka, a cikin lokaci kadan, mu ka murkushe su baki daya, ya zama a yau, babu inda ake jin motsinsu a fadin jihar Kaduna.
Bayan mun samu nasarar murkushe wadannan bata – gari, mai girma gwamnan jihar Kaduna da kan say a jinjina ma na, tare da sa ma na albarka, na wannan mihimmin aiki da mu ka aiwatar a fadin kananan hukumomin jihar Kaduna.Kuma tun da mu ka samu sa albarkan mai girma gwamnan jihar Kaduna sai mu ka samu kwarin gwiwar kara tashi tsaye, na fito – na – fito da duk dai –daikun bata – gari da suke labe a fadin jihar Kaduna.
Ka dauki misali da karanan hukumomin Sabon Gari da Zariya, kowa ya san an samu mafita a yawan aikata manya da kuma kanan laifuffuka da suke faruwa a wadannan kananan hukumomi da kuma sauran kananan hukumomi na jihar Kaduna, domin yadda jami’anmu na Zariya da Sabon gari da na Kaura da na Birnin Gwari ke aiki haka na ko wace karamar hukuma suke yi, ka ji dalilan samun nasarorin da na bayyana ma ka mun samu sa shekara ta 2018, da ta gabata.
Kamar wasu bangarori ku ka samu nasarorin?
Bangarori da mu ka samu nasarori suna da yawa, muhimmai su ne, kananan yara ma su kwace wa al’uuma wayoyin hannu [GSM], da ‘yan sara – suka da ‘yan sane da ma su fasa gidaje da ma su fasa shaguna da satar shanu da satar abubuwan hawa, kamar motoci da Babura da kuma manyan laifuffuka da suka hada da fashi da makami da fyade da kuma luwadi da ake yi wa kananan yara maza da kuma mata.
Kuma dole mu jinjina wa gwamnan jihar Kaduna da kuma shugaban karamar hukumar Sabon Gari, na yadda duk abin da mu ka nuna mu na bukata da suka shafi ayyukanmu, ana ba mu a kan lokaci, wannan ya na kara ma na kwarin gwiwar fuskantar tabbatar da tsaro a jihar Kaduna, wanda ya haifar da duk wani mai aikata laifi, a jihar Kaduna ya na tsoron yin gaba da gaba da jami’anmu.
Da rana ko da daddare ku ka fi samun nasarar ayyukanku?
Ai duk lokacin da mu ka motsa domin gudanar da ayyukanmu, cikin ikon Allah, mu na samun nasara ko kuma in ce nasarori, domin mu na da ma su leken asiri a cikinmu, da zarar mun tashi daga ofishinmu, mun san inda mu ka dosa, da zarar mun je inda mu ka saw a gaba, sai ka ga mun yi ma su aikata laifi kamun kazar kuku, musamman ‘yan shaye –shaye da sauran wadanda na ambata ma ka a baya.
Wasu lokaci ku ke iwatar da ayyukanku?
Ai duk inda ka ga ofishinmu, mu na aiki na tsawom sa’o’I 24, wato duk lokacin da ka je za ka same mu a ofis, wasu kuma suna wasu wurare, domin gudanar da ayyukan da ma su leken asirimu suka gano.
A baya kuna kukan in kun damke ma su laifi, daga baya ana sakinsu, musamman a shekarar da ta gabata, an samu mafitar wannan matsala?
Babu ko shakka, an samu mafita, a wasu lokuta mu na aiki da sauran jami’an tsaro, wannan na cikin dalilan da suka sa wannan matsala ta zama tarihi.
Kuma zan manta ba, mun taba kama ma su garkuwa da mutane, mai girma gwamnan jihar Kaduna da kansa ya shaida wa sifeton ‘yan sanda na Nijeriya, cewar mu na aiki tukuru, to tun da gwamna da kansa ya yaba ma na, ai ka ga baun ku ka kuma kenan.
Ina aka tsaya a batun satar shanu da a baya matsalar ta zama rowan dare?
Batun satar shanu babu wannan batu, domin a babu wannan matsala a daukacin kananan hukumomin jihar Kaduna 23, an samu wannan nasara ne, domin wkarin gwiwar da mai girma gwamnan jihar Kaduna ya ba mu da kuma sauran jami’an tsaro da suke jihar Kaduna.
Ka gamsu da gudumuwar da ma su hannun murza – zare ke ba ku a fadin jihar Kaduna ?
Lallai na gamsu, babu shakka al’umma nab a mu gudunmuwa da suka shafi maboyan bata – gari da kuma wasu abubuwa da suke zaburar da mu na ayyukan da mu ke yi.
A baya ka yaba wa gwamnan jihar Kaduna, shugaban majalisar Kaduna daga karamar hukumar Sabon Gari yak e, ya na tallafa ma ku kuwa?
Babu ko shakka, in ka cire mai girma gwamnan jihar Kaduna, babu wanda ke tallafa wa wannan hukuma a jihar Kaduna, kamar shugaban majalisar jihar Kaduna, Alhaji Aminu Abdullahi Shagali,domin har mota ya ba mu, domin mu samu saukin gudanar da ayyukanmu.
Ga shi mun shiga sabuwar shekara ta 2019, wasu ayyuka za ku fuskanta kuma?
Babban aikin da za mu fuskanta shi ne, kara tashi tsaye na tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar jihar Kaduna da kuma dukiyoyinsu, sai dai mu na kira ga iyaye a jihar Kaduna su kara sa ido ga yaransu maza da kuma mata, domin akasarin ma su aikata laifuffuka a yau yara ne matasa, sai dai a batun day a shafi fyade da luwadi, an fi samun ma su yawan shekaru.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!