Connect with us

LABARAI

Rundunar Soji Ta Karyata Batun Rufe Titin Maiduguri Zuwa Damaturu

Published

on

Rundunar Sojin Nijeriya a yau Laraba ta karyata labarin nan da ya yadu a kafafen sada zumunta cewa sun rufe babban titin Maiduguri zuwa Damaturu gaba daya.

Kanal Onyema Nwachukwu, mataimakin Daraktan hulda da jama’a na Sintirin LAFIYA DOLE, shi ne ya bayyana hakan, inda ya kara da cewa; ba su rufe hanyoyin domin hana motoci wucewa ba kamar yadda aka rika yadawa a shafukan sada zumunta.

Nwachukwu ya ci gaba da cewa; rundunar ‘Operation LAFIYA DOLE’ sun gudanar da bincike ne a wadansu yankuna dake hanyar domin kare rayukan al’umma da kuma tabbatar da matafiya ba su fuskanci wata matsalar tsaro ba.

Ya kara da cewa; batun cewa sun rufe hanyar gaba daya, wannan sam ba gaskiya bane. Ya ce; “abin da ya faru shi ne, mun gudanar da bincike ne a wadansu yankuna dake yankin domin rahoton da muka samu na yadda aka wadansu suna sintirin a hanyar da ake zargin ‘yan Boko Haram ne. Wannan binciken mun yi shi ne domin kare rayukan matafiya da sauran al’umma.” Inji shi.

Nwachukwu a kasrhe ya yi kira ga jama’a da su rika ba su hadin kai wajen gudanar da ayyukansu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!