Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Kwastam Ta Yi Babban Kamu A Jihar Edo

Published

on

Jami’an hukumar kwastam na Nijeriya reshan ‘Zone C’ da ke Owerri jihar Imo, sun kama motar bas kirar Toyota Hiace dauke da buhun shinkafar kasar waje guda 25 mai nauyin kilo 50 tare da wake a garin Benin cikin jihar Edo. An bayyana cewa kudin harajin shankafan da kuma motar bas din zai kai naira 7,100,000. Da yake yi wa manema labarai karin bayani narar Talata a sito din hukumar da ke Aduwawa cikin garin Benin, shugaban sashi na hukumar Mista Kayode Olusemire ya bayyana cewa, an samu wannan nasara ne sakamakon binciken sirri da hukumar ta yi. Olusemire ya kara da cewa, “Ban san dalilin da ya sa ‘yan Nijeriya suka tsunduma cikin wannan haramtacciyar kasuwanci na fasakauri ba, duk da kokarin da gwamnatin tarayya take yi wajen habaka masana’antu masu nika shinkafar gida a cikin kasar nan. “Duk da irin bashin da gwamnatin tarayya ta ba wa manoma ta hannun ma’aikatu da kuma hukumomi domi noman shinkafa mai yawa, amma masu fasakaurin suna kokarin rushe wannan lamari. “ Mu dai ‘yan Nijeriya ne duk da irin son shinkafar kasar waje da muke yi, ta mu na gida tafi gina jiki kuma tafi bayar da lafiya sannan tafi arha. “Ya kama ta mu sani cewa shinkafar kasar waje tana raunata lafiyar jikinmu, sakamakon dadewar da buhun shinkafar yake yi ke sa dandanonta ya gushe, amma duk da haka mutane suna ci gaba da san ta.”
Yin fasakwaurin yana raunata tattalin arzikin kasa, Olusemire ya shawarci masu shigowa da kaya da su tunga ziyartar hukumar ta safin yanar gizo, domin samun bayanan kayayyakin da gwamnatin tarayya ta hana shigowa da su cikin kasar nan. Ya sha alwashin cewa hukumar kwastam za ta ci gaba da kwace duk wani kayayyakin da aka yi fasakwaurinsu, indai har masu fasakwaurin basu daina gudanar da wannan haramtacciyar kasuwanci ba. Olusemire ya kara da cewa, “Ina bakin cikin irin asarar kudin da masu fasakwauri suke yi duk lokacin da aka kwace abin da suka yi fasakwaurinsa. “Wannan irin mutane ne wadanda basu son tattalin arzikin kasa ya habaka. Duk da haka, ba za mu gaji ba wajen kokarin ganin aikin hukumar kwastam ya inganta. “Idan masu fasakwaurin sun dauki mataki daya wajen ci gaba da haramtacciyar kasuwancinsu, to mu za mu dauki mataki guda hudu wajen durkusar da kokarin su.”
Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya musamman masu gudanar da fasakwauri, su canza wannan haramtacciyar kasuwancin zuwa halattarciya. Ya kara da cewa, bunkasar tattalin arzikin kasa shi ne matakin farkon na dukkan al’umma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!