Connect with us

MANYAN LABARAI

Malamai Nunar Rana Ke Haddasa Rikici A Nijeriya – Sarkin Musulmi

Published

on

Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’Ad Abubakar III ya ce, malaman da ba su cika malamai ne ba suke haddasa rigingimu a kasar nan ta hanyar wa’azozin su.
A cewar shi, suna yin wa’azozi ne na tsokana da tayar da hargitsi ga mabiyan su.
Ya bukaci Musulmai da Kiristoci na kasar nan da su rika girmama Addinin junan su, yana mai cewa, ba wanda za a tilasta wa ya rabu da Addinin shi ya zama Kirista ko Musulmi.
Sultan, wanda Sarkin Keffi, Alhaji Shehu Chindo Yamusa III, ya wakilce shi, ya bayyana hakan ne a Jiya a garin Auchi, Jihar Edo, a wajen bikin ranar Auchi.
Sultan din ya yi nuni da cewa, ba bu tilasci a cikin Addini.
“Kamata ya yi Musulmai su nemi ilimi domin su fahimci yanayin da ake ciki, su san yanda ya kamata su fuskance shi. Abin takaici ne yanda Musulmai suke daukan wani nau’in ilimin, alhalin ilimin Musulunci shi ke sama da komai, domin shi zai taimaka mana mu fahimci abin da ake nema daga garemu,” in ji shi.
Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su marawa gwamnatin tarayya a kan yakin da take yi da rashin tsaro da matsalar cin hanci da rashawa domin amfanin kasarmu, domin kowa zai amsa sakamkon abin da ya aikata.
A kan zaben 2019, Sultan ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da duk wasu hanyoyi na aikata magudin zabe da wasu abubuwa marasa kyau, su yi zabe a bisa la’akari da ‘yan takaran da suke zaba a bisa son su.
“Ina rokon ku da ku yi watsi da duk wasu sabanin da ke tsakaninku, ku aikata abin da zai hada kanmu a matsayin ‘yan kasa guda. Tilas ne mu kasance masu yafiya, sai Allah Ya gafarta mana,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!