Connect with us

SIYASA

Mataimakin Shugaban PDP Na Kasa, Ya Koma Jam’iyyar APC

Published

on

Shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari ya amshi bakwancin wasu mambobin da suka fice daga cikin jam’iyyar PDP, ciki kuwa har da tsigeggen mataimakin shugaban ja’iyyar PDP na kasa a shiyyar Arewa, Sanata Babayo Garba Gamawa da kuma wani daga cikin mambobin majalisar amintattu na jam’iyyar PDP, Kaulaha Aliyu, wanda suka dawo cikin jam’iyya mai mulki (APC).
NAN ta labarto cewar wadanda suka fice daga PDP gami da shiga cikin APC din, sun samu rakiyar gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abubakar, inda suka yi ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsawon mintuna 35.
Da yake jawabi ga ‘yan jarida a fadar shugaban kasa, Gwamnan jihar Bauchi, Muhammadu Abubakar ya nuna gayar farin cikinsa a bisa wannan ci gaban da jam’iyyar APC ta samu, ya shaida cewar sabbin kamu na jam’iyyar sun kawo wa Buhari ziyarar ne domin nuna goyon baya wa shugaban kasa Buhari.
Abubakar, ya kuma jinjina wa Gamawa da Kaulaha a bisa daukan wannan matakin da ya dace a daidai lokacin da ya dace, “za ku iya gani kuma za ku iya fahimtar yadda na ke cike da farin ciki da annashuwa, zan je na yi barci idona biyu cike da shauki,” Inji shi
A tasa bangaren, Alhaji Babayo Gamawa ya bayyana cewar sauya shekar da yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC bai da wani alaka da dakatar da shi da PDP din ta yi, ya ce ya yi hakan ne kawai don soyayyar da yake yi wa Nijeriya.
Ya kuma bayyana cewar, tabbas PDP sai ta yi nadamar dakatar da shi daga ofishinsa na mataimakin shugaban jam’iyyar.
“A matsayina na dan Nijeriya ina son ganin kasata a cikin kyakkyawar yanayi, kuma ina son na kare mutunci da kimar kasa ta, don haka ina sha’awar ganin ci gaban kasata na habakuwa.
“A matsayi na dan siyasa, ni ina yin siyasa ne ba da damuwa ko hargitsi ba. duk lokacin da wani abu ke faruwa, daidai ne ko akasinsa ni ba zan ce ga yadda ke tafiya ba. a matsayinku na ‘yan jarida, kuna sane da halin da PDP take ciki a yau, kai ka ji fa, a bisa zargi ne suka dakatar da ni.
“Ni ko kadan ban yi nadamar fita daga jam’iyyar PDP ba, domin ita PDP sai ta yi nadamar daukan matakin da ta yi a kaina da yardar Allah,” Inji shi
Ya kuma misalta dakatarwar da PDP ta yi masa a mtsayin rashin bin mataki na demokradiyya da kuma rashin bin dokoki.
Shi kuma a nasa bigiren, Kaulaha Aliyu, ya shaida cewar ya dawo APC ne domin tabbatar da nasarar zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben da ke tafe.
A wata sabuwar kuma a dai ranar Litinin ne shugaban kasar ya kuma amshi wasu da suka dawo cikin jam’iyyar APC daga shiyyar Arewa maso gabas ciki kuwa har da Umar Bukar Bolori, a fadar shugaban kasa.
Sauran wadanda suka dawo APC din sun hada da tsohon gwamnan tsohowar jihar Borno, Alhaji Mohammed Goni, da kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Adamawa, Alhaji Saad Tahir.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!