Connect with us

MANYAN LABARAI

Nakasassu Sun Ayyana Goyon Baya Ga Buhari

Published

on

Mai ba shugaban kasa Muhammdu Buhari shawara a kan mutane masu fama da nakasa, Dakta Samuel Ankeli ya bukaci yan Nijeriya su ba shugabn kasa dukkan goyon bayan a ya ke bukata don guna kasa da kawo cikakken ci gaba.
Ya gabatar da wanna bukatar ne jiya a garin Abuja a yayin da yake kaddanar da kwamitin yakin meman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari bangaren mutane masu fama da nakasa, an shirya kwamitin ne don ta nema wa shugaba Buhari goyon baya a zaben dake tafe 2019.
Ankeli ya yaba wa shugaba Buhari a kan kulawar da yake yi wa mutane masu fama da nakasa, don kuwa a shekarun baya an mayar da su saniyar ware ba a kulawa da su gaba daya a harkokin gudanar da mulki.
“A karon farko a tarihin kasar nan mun samu gwamnati mai kulawa da mu, muna godiya ga shugabancin jam’iyyaar APC da suka mahimmatar damu. Ina mai sanar daku cewa, ya yi shawarar bamu daman na musamman da zamu bayar da gudumawarmu a kan yadda za a gudanar da yakin neman zaben Shugaba Buhari a wannan zaben dake tafe.
“Amma bayani ya nuna cewa, mutane masu nakasa suka na matukar kwazo a kan dukkan abin da suka sa a gaba, saboda haka zamu shiga sako sako don nema wa shugaba Buhari kuri’a a dukkan fadin tarayya kasar nan, muna kuma da kwarin gwiwar cewa, muna da mutane da yawan gaske a, a kan haka ne muke yi wa shugaban kasa alkawarin kuri’a miliyan 25 a zaben dake tafe.”
Ya kuma kara da cewa, gwamnatin jami’yyar APC ta samar da ofishin mai ba shugaban kasa a kan hakokin masu nakasa don taimaka wa jamam’a masu fama da nakasa a saboda haka zamu fito kwamnu da kwarkwatarmu mu jefa masa kuri’a gaba daya, hakan zai taimaka mana samun dokar da zai tallafa wa rayuwar mutane masu fama da nakasa a Nijeriya.
Ya kuma yaba wa hukumar zabe ta INEC, in da ya ce, suna gabatar da ayyukan da ya kamata, hakan kuma yana kara kwarin gwiwa ga jama’ar kasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!