Connect with us

KASUWANCI

Shugaban Babban Bankin Duniya Zai Sauka A Watan Fabrairu

Published

on

A ranar Litinin data wuce, Jim Yong Kim, Shugaban Babban Bankin Duniya ya yi shelar cewar, zai yi murabus daga shugabancin sa bayan ya shafe sama da shekaru shida yana kan karagar shugabancin Bankin da masu ruwa da tsaki dake bankin suka bayar da gagarumar goyon baya wajen wanzar da shirye-shirye da suka sanaya bankin ya ci gaba da zamowa mai karfin gaske a idon duniya. A cikin sanarwar da Kim ya fitar ya yi nuni da cewar, ba karamar martaba bace a gare da ya samu ya shugabanci bankin mai dimbin tarahi a duniya ba, shugabannin da dama da suka shugabanci bankin a baya sun yi aiki tukuru don ganin sun bayar da gydunmawar su wajen rage talauci, inda ya yi nuni da cewar, bankin a yanzu yafi mahimmanci fiye da a baya ganin cewar talakawa sunyi na’an da bankin, musamman wajen yaki da canjin yanay annoba, yunwa da kuma ci gaba da ake yi na tallafawa yan gudun hijira. Ya sanar da cewa, shugabantar bankin da ya yi ya tai.aka wajen daukaka matsayin bankin duk da tsaka mai wuya na kalubale da ya fuskanta kuma hakan ya zamo masa wata alfarma a rayuwar sa. Acewar sanarwar, a karkashin shugabancin Kim tare da goyon bayan kasashe wakilai 189 dake karkashin bankin, a 2012 bankin ya kirkiro da abu biyu da yake son imma buri a kai na rage radadin talauci kafin 2030 da kuma inganta rayuwar kashi 40bisa dari na kasashe masu tasowa. A karshe ya ce, masu ruwa da tsai sun bayar da gagarumar goyon baya a kan matakan da bankin ya dauka do kara daukaka martabar bankin a idon duniya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!