Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Fashi Sun Farmaki Shugaban Kungiyar Kwadago Na Jihar Benuwai

Published

on

‘Yan fashi da makami sun farmaki shugaban kungiyar kwadago na jihar Benuwai mai suna Godwin Anya. Ya dai kubuta daga wannan farmaki ne, yayin da suka harbi matarsa. Anya shi ne ya bayyana wa manema labarai haka a hiran da suka yi da shi ta wayar tarho, ya bayyana cewa bai halacci zanga-zangar kunciyar ba na ranar Talata. Anya ya ce, bai jagoranci zanga-zangan bane, sakamakon harbin da ‘yan fashi suka yi wa matarsa. Da yake bayanin yadda ya shiga hannun ‘yan fashin, shugaban kungiyar na jihar ya bayyana cewa, ya je kauyensu ne a Ushongo domin halartar bikin kirsimeti da na sabowan shekara, a nan ne ‘yan fashin suka farmake shi. A cewarsa, da misalin karfe 12 na dare ne lokacin da ake gudanar da addu’o’in shiga sabowar shekara a cikin gida, sai ‘yan fashin su biyar suka farmake mu. “Sun same ni a cikin daki inda suka amsa naira 750,000 kudin makarantar yarana tare da amshe mana dukkan wayoyinmu. Na kai rahoton faruwar lamarin ga ofishin ‘yan sanda da ke Ushongo,” in ji Anya.
A halin yanzu, shugaban kungiyar na jihar sun gudanar da zanga-zanga a kan manyan titin da ke Makurdi bisa karancin albashi a ranar Talata.
An gudanar da wannan zanga-zangan ne a gidan gwamnati, inda shugaban hadaka na kungiyoyi na Ojotu Ojemu ya wakilci shugaban kungiyar kwadogon, inda ya yi kira ga gwamnan a kan ya tabbatar da cewa an cafke wadannan ‘yan fashi. Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro su kare shugaban kungiyar na jihar, ya bayyana cewa biyan mafi karancin albashi na naira 30,000 ya zama doka.
Da yake magana a kan zanga-zangan, shugaban kungiyar na kasa Ayuba Wabba wanda ya samu wakilcin Dakta Success Leke wanda shi ne mai duba asusun kungiyar na kasa, ya shawarci gwamna Samuel Ortom ya amince da bukatar kungiyar na aiwatar da sabon tsarin karancin albashi.
Ortom yana tausaya wa ma’aikatan a kan wahalar da suke sha, ya bayyana musu cewa idan suna gudanar da aikinsu yadda ya kamata, to nan take zai aiwatar da sabon tsarin albashin. Sannan ya yi kira ga gwamnatin tarayya a kan su kara duba tsarin rarraba tattalin arziki. “Gwamnatina tana ba wa albashin ma’aikata mahimmanci, wannan shi ne abin da muke yi,” in ji Ortom.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!