Connect with us

LABARAI

2019: Wajibi Ne A Taka Wa Sayar Da Katin Zabe Birki, In ji Saraki

Published

on

Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya shawarci masu ruwa da tsaki kan babban zaben 2019 da ke tafe da cewar su tashi tsaye domin taka wa matsalar sayar da katin zabe birki domin hakan zai kai ga shawo kan munanan dabi’un wasu gurbatattun ‘yan siyasa da ake zargi da sayen katin zabe na dindindin (PBC) a hanun masu zabe.
Saraki ya yi bayanin haka ne, biyo bayan ikirarin da shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Mahmoud Yakubu ya yi a ranar Laraba da ke cewa, wasu ‘yan siyasa na sayen katinan zabe na dindindin a hanun masu zabe.
Shugaba Saraki ya nemi INEC ta gaggauta dakatar da wannan mummunar dabi’ar tun da har an samu bayanai faruwarsa, yana mai shaida cewar da akwai gayar bukatar a gaggauta bijiro da hanyoyin dakile wannan lamarin cikin gaggawa domin ganin ‘yan siyasa masu sayen kuri’un basu kai ga cimma muradinsu ba.
Dukkanin wadannan jawabai na Bukola Sarakin, na zuwa mana ne ta cikin kwafin sanarwar manema labaru da mai magana da yawun shugaban majalisar Dattawan, Yusuph Olaniyonu ya sanya wa hanu hadi da aikewa gidajen jaridu a jiya, ya ce muddin aka yi sakaci wannan lamarin ya ci gaba da faru zai kawo gagarumar cikas din da ka iya janyo barazana wa babban zaben 2019, ya ce kuma ta hanyar dakkatar da wannann lamarin za a iya samun nasarar gudanar da zabe mai nagarta.
A cewar Abubakar Saraki, “Za mu ci gaba da tabbatar da dukkanin wani magudi da murdiyar zabe bai samu gindin zama ba, gabanin da kuma bayan babban zaben. Kuma za mu ci gaba da yin hakan har sai ranar da aka sanar da sakamakon zabe. Don haka ne ma muka dugufa wajen ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali da tsanake da kuma tabbatar da fuskantar dukkanin wata barazanar da muke ganin zai kawo cikas wa tabbatar da adalci da gudanar da sahihin zabe, kamar yadda shugaban zaben ya yi, dukkanin masu ruwa da tsaki su hada hanu waje guda domin a samu nasarar gudanar da zaben nan cikin kwanciyar hankali kuma ba tare da makudi ba.
“Dukkanin masu ruwa da tsaki dole ne su farga kuma su tashi tsaye domin ganin an dakile wannan danyen aikin na wasu gurbatattun ‘yan siyasa masu sayen katinan zabe a wajen jama’a. Muna da bukatar hada karfi da karfe wuri guda don kawar da wannan, ina da yakinin masu ruwa da tsaki suna da gagarumar rawar da za su iya taka wajen ganin wannan aika-aikar bata kai ga cimma nasara ba, sannan, za kuma a iya kirkirar wata hanya ta daban da ba lallai su masu sayen kuri’un su kai ga gano ba domin shawo kan matsalar cikin ruwan sanni,” Inji Saraki.
Saraki ya na mai kara da cewa, a dan sauran makonni shida da suka rage na fara zaben farko da ke tafe, da bukatar INEC ta yi wani shiri na gaggawa da zai jawo hankalin masu ruwa da tsaki don yin wani tsari da zai kai ga shawo kan kowace irin matsala domin dai a samu yin zabe mai cike da adalci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!