Connect with us

TATTAUNAWA

Abin Da Ya Sa Na Fi Cancantar Zama Gwamnan Katsina A 2019 –Jikamshi

Published

on

ALHAJI ABUBAKAR HALILU JIKAMSHI, Shi ne xan takarar Gwamnan Jihar Katsina a qarqashin jam`iyyar National Rescue Movement (NRM), wanda ya yi ritayi a matsayin Babban Darakta a Hukumar Birnin Tarayya Abuja, sannan Tsohon Mataimakin Shugaban Qungiyar Masu Nazarin Filaye da Safiyo na Qasa. A cikin tattaunawarsa da Leadershi A Yau a Abuja wannan makon, Jikamshi ya jaddada yaqininsa na cewar shi ne wanda ya fi kowa cnacantar zama Gwamnan Jihar Katsina a 2019 da gwamnatin jihar ta gaza tavuka abin a zo a gani tsawon lokaci. Sannan ya ce Katsina zata fi kowace jihar samun nasarar dimokuraxiyya a qarqashin jagorancinsa idana aka zave shi gwamnan jihar a wannan karon dfa sauran batutuwa da dama. Ga yadda tattaunawar ta kasance kamar haka:

Da farko idan Allah Ya sa ka zama Gwamnan Jihar Katsina, mene ne zaka yi wanda zai bambanta da yanayin da ake ciki da zai inganta rayuwar jama`ar jihar?
To da farko, zan yi aiki da masu son ci gaba, don inganta rayuwar al’ummar jihar waxanda zamu yi aiki tare don qaddamar da bunqasa harkokin tattalin arziqi ta hanyar kafa masana’antu da janyo hankalin masu zuba jari su zo su kafa kamfanoni ta yadda za a samarwa matasanmu ayyukan yi, wannan shi ne babban abin da ya dame. Domin a kullum muna horar da xalibai daga makarantun sakandare da jami’o’i to amma babu ayyukan yi.
Ina zaune a Abuja amma na san yadda takwarorinmu na Kudu suke gudanar da harkokinsu. Wasu Gwamnonin Kudancin Najeriya suna yi wa jama’arsu aiki tuquru don samar da muhallin gina masana’antu wanda hakan zai taimaka wa matasa wajen rage rashin ayyukan yi wannan yana xaya daga cikin burinmu a Katsina. Sannan katsina ce da Allah Ya albarkace ta da ma’adinai sannan ga kuma qasar noma, wanda wannan gwamnati ta gaza maida hankali akansu. Sai ya zama jiya i yau, babu ci gaba. Kuma idan ka duba yawanci rashin aikin yi ga matasan nan ne yake haddasa mafi yawan tashe-tashen hankula da sauran fitintinu na Boko Haram da satar mutane da bangar siyasa. To zamu wani abu cikin gaggawa don maida Katsina sabuwar jiha.

Waxanne irin tsare-tsare zaka fito da su don cimma wannan quduri idan ka samu kujerar?
Zamu gayyaci waxanda suka dace don tabbatar da ba a dogara da kason kuxin da gwamnatin tarayya ta ke bamu. Zamu fuskanci harkokin ilimi da noma da kuma samar da ayyukan yi kamar yadda na gaya maka. Mu mayar da matasanmu abin alfahari, domin suna da fasahar, amma an qi a ba su dama. Sannan zamu janyo hankali masu zuba jari zuwa Katsina don sarrafa albarkatun da muke da su na ma’adinai da kuma harkokin noma.

Wannan jam’iyyar na xaya daga cikin sababbin jam’iyyu waxanda aka yi wa rajista wanda zata tunkari jam’iyya mai mulki ta APC a Katsina, wane dama NRM ke da shi na samun nasara a zaven da ke tafe?
Taken jam’iyyar tamu ma shi ne Allah ke bada mulki watau ‘Power Comes from God’ kuma mun yarda cewa, Allah ke bada mulki lokacin da Ya ke so ga wanda Ya ke so, Ya kan ba duk wanda Ya ke so kuma zai iya hana kowa duk dukiyar da mutum ya mallaka ko jama’a. Kuma manufar mu ita ce mu yi wa jama’a hidima ba wai mu azurta kanmu ba. Kuma a makon mai zauwa zan qaddamar da yaqin neman zavena a Katsina, wanda zamu haxa kai da dukkan masu kishin jihar da matasanmu don tabbatar da cewa mun kai ga nasara. Domin kowa shaida ne cewa APC a Katsina ta gaza bisa manufofi da kuma qudurin sanuyin da al’umma suka zave ta akansu. APC ta gaza, ai da muna cikinta, tun ma ANPP har muka zo APC, amma abin takaici sai ya kasance sauyin da al’umma ke zaton samu bai yiwu ba, wannan shine dalilin da ya sanya muka kafa wannan jam’iyya qarqashin jagorancin Sanata Xansadau don ceto qasar nan daga halin da ta ke ciki ba ma jihar Katsina kawai ba.

Akwai zargin sayen quri’a wanda ke zam qalubale wajen samar da ingantaccen zave. Ta ya ya kake ganin za a daqile hakan don tsaftace zave a Najeriya?
Wannan abu me sauqi ne, akwai buqatar ilmantar da masu kaxa quri’a. Masu kaxa quri’a su sani cewa, ’yan siyasa na iya amfani da kuxi wajen sayan katin kaxa quri’a, a maimakon a yi amfani da kuxin wajen qaddamar da abubuwan more rayuwa ga al’umma, idan har hakan ya faru masu kaxa quri’a ba zasu iya gabatar da qorafinsu ba saboda sun sayar da quri’unsu ba. Ya kamata gwamnati ta zage damtse wajen tabbatar da sahihin zave a faxin qasar nan, wannan zai rage sayan quri’a a zavuka. Kuma alhamdulillahi al’ummarmu a kullum suna gane illolin yin hakan.

Jihar Katsina jihar Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ce, sannan kuma mai mulkin jihar. Ta ina zaka fuskanci wannan qalubale don ganin ka samu nasara a zaven 2019?
Eh, haqiqa faxuwar Buhari a wannan takarar ba qaramin aiki ba ne, saboda irin qaunar da jama’ar jihar suke yi masa, amma a zahiri da ace ana yin dimokuraxiyya irin ta qasashen da suka cigaba ba abu ba ne me wahala kayar da shi, ba wai shi karan kanshi ba, amma sauran muqarraban gwamnati, kuma gwamnatin yanzu ta gaza ta fannoni da dama. Domin ’yan Najeriya na cikin wahala, jama’a basa tsammanin irin abin da suke fuskanta a yanzu na wahalhalun rayuwa da rashin tsaro. Abin mamakin ana shi ne Ministan Tsaron Najeriya xan Arewa maso Yamma ne, amma har yanzu ban san me yake yi akan muqaminsa ba ganin irin wannan munanan ayyukan ta’addanci dake faruwa a qasar.

Gwamna Masari tsohon kakakin majalisar tarrayya ne kuma jama’ar jihar na cewa, yana biya masu buqatunsu. Me yasa kake qalubalantarsa a wannan karon?
Ba zan iya cewa, bai tavuka komai ba. A tunani na yana xaya daga cikin mutumin da yasa Buhari ya gaza. Ya kamata ka ziyarci Jihar Katsina don ka saurari koken talakawan jihar. Ana buqatar shirin wayar da kan al’umma don fitar da su daga cikin qangin wahalar da suke ciki a yanzu. Jihar Katsina na cikin jihohin da take da masu ilimi a qasar nan, mafi yawan tsofaffin shugabanninmu daga nan suke, amma ba inda muka dosa har yanzu.
Ako da yaushe zamu ce, zamu ilmantar da jama’armu amma ba mu da wani tanadi da muka yi wa rayuwarsu nan gaba. Sai dai mu yi ta cewa, muna son samar da ayyukan yi, amma ba ma tanadar da yanayin da matasa zasu samu ayyukan yi. Ba a horar da su akan su samu wasu dama da zasu iya dogara da kansu, sai dai kawai muna samar da qofa ga masu nishaxantarwa kawai.
Akwai buqatar ka zauna a Jihar Katsina don kasan halin da jama’ar jihar ke ciki. A jam’iyyarmu babban burinmu shi ne ceto al’umma daga halin durqushewar walwalar tattalin arziqi da yake koma samun koma baya.
Ba su qoqarin daqile qalubalen rashin aikin yin matasa daga tushe, wanda ya baiwa ’yan Boko Haram qofar horar da mambobinsu. Ba a kama waxanda suke taimaka masu, akwai alamar tambaya ganin Ministan Janar na soja ne, ya kamata ace ya yi aiki fiye da haka.

Kana da yaqinin cewa, Hukumar Zave INEC zata iya gudanar da sahihin zave a 2019?
Ina fatan hakan, saboda an yi min maguxi lokacin da nake takara. Na san abin da hukumar zaven zata iya aiwatar wa da kuma irin hukuncin da zasu iya yanke wa, ina farin cikin cewa, Alqalin Alqalan Najeriya Mai shari`a Onoghen ya gargaxi sauran alqalan Najeriya da su zage damtse a ayyukan su, kuma mu na da yaqinin cewa zasu yi adalci a zave na gaba.
Duk da haka shugaban hukuar zave mai zaman kanta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi alqawarin cewa, hukumar zata gudanar da sahihin zave a Najeriya. Saboda an samu darasi daga zavukan jihohin Osun da Ekiti.
Koda yake sayan quri’a na taka muhimmiyar rawa, a jihar Katsina an gudanar da zaven cike gurbi, sayan quri’a nada muhimmanci a jihar kuma an fahimci hakan, saboda ba na Katsina lokacin zaven amma na samu rahoton cewa, lokacin gudanar da zaven idan me kaxa quri’a ya fahimci za a biya shi daga cikin wakilan jam’iyyun toh nan take sai ya nuna masa abin da zai kaxa wa quri’a don ya biya shi. A NRM ba mu da isassun kuxaxe da zamu iya sayan quri’a kuma ba zamu iya yin qarya akan hakan ba.

Kawo yanzu ka gamsu da yadda jama’a NRM ke karvuwa a Katsina?
Jama’a da dama nata sauya jam’iyya, amma masu faxa aji basa shigo wa jam’iyyarmu, saboda su a tunanin su shi ne ta hanyar Gwamnati ne kaxai zasu iya samun kuxi. Waxannan mutanen basa amfani da tunaninsu, sannan sukan manta da ranar tashin qiyama. Duk mabiyan mu da suka halarci kamfen xinmu a Gusau zasu harlara a Katsina, wannan zai nuna yadda jama’a ke goyon bayanmu kuma hakan zai nuna cewa a shirye suke da kawo sauyi.

Ko akwai alamar yin zaven 2019 ba tare da wani rikici ba?
Wannan Allah ne kaxai ya sani, amma wani lokaci ya danganta ga yadda ake gudanar da zaven ke bada damar yin rikici, saboda idan akwai sayan quri’a, da satan akwatin zave da kuma tozarta masu kaxa quri’a ga wanda lamarin ya shafa. Muna addu’a gudanar da zaven lafiya ba tare da wani rikici ba a duk yankunan qasar a 2019. ’Yan Najeriya duk sun san hanyoyin da zasu bi don kauce wa aikata laifi, kuma muna fatan irin waxannan zasu tabbatar da an yi zaven 2019 ba tashin hankali.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!