Connect with us

LABARAI

Jirgin Kasa Ya Yi Hadari A Legas

Published

on

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Kasa ta tabbatar da mutuwar mutum daya da safiyar jiya a wani hadarin jirgin kasa da ya auku a layin dogo da ya ratsa Unguwar Agege a birnin Ikko. Babban Jami’in Hukumar na Gunduma, ya shaida wa manema labarai cewa mutumin da ya mutun ya riga gidan gaskiya ne a Asibitin Hukumar da ke Ebute Meta lokacin da ake ma sa magani.

“Muna ci gaba da kokarin ganin komai ya daidaita a wurin da al’amarin ya auku”, in ji shi A cewar Hukumar Sufurin Jiragen Kasan, hazikan jami’anta sun dukufa wurin ganin an sake dawo da jirgin layinsa da ya goce a kai tare da gyara abubuwan da suka lalace. Ta tabbatar da cewa, ba da jimawa jirgin zai ci gaba da zirga-zirga da zarar an kammala gyara.

Kamfanin Dillancin Labarun Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa dubban fasinjoji ne suka tsallaka rijiya da baya a yayin da jirgin ya yi hadari a layin dogo da ke Ashade a Unguwar Agege da ke birnin Ikko Hadarin jirgin dai ya auku ne da misalin karfe 7 na safe inda wasu fasinjojin cikin jirgin suka ji raunuka. Ba da jimawa ba da aukuwar lamarin, jami’an tsaro suka killace wurin domin tabbatar da barayi ba su ci karensu ba babbaka ba a wurin, tare da yin gaggauwar daukar marasa lafiya zuwa Asibiti.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!