Connect with us

SIYASA

Ko Sanata Galaudu Zai Samu Nasarar Zama Gwamnan Kebbi A 2019?

Published

on

A yayin da babban zaben 2019 ke kara gabatowa kusa, masu fashin bakin al’amurran siyasa da al’ummar Jihar Kebbi suna da ra’ayin zaben da za a gudanar a jihar zai yi matukar zafi da daukar hankalin jama’a fiye da zabukan da suka gabata.
A cewar masu irin wannan ra’ayin tuni jam’iyyar APC wadda Gwamna Abubakar Atiku Bagudu zai sake yi wa takara a karo na biyu ta shiga cikin rudani a dalilin gagarumar karbuwar da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta samu a jihar.
Fitaccen dan siyasa mai kima, tasiri da farin jini Sanata Isa Galaudu ne zai auna tsawonsa da Gwamna Bagudu lamarin da wasu da dama ke gani a matsayin zaben da za a yi fafatawar karon battar karfe.
Wasu na ganin yawaitar canza sheka daga APC zuwa PDP a Kananan Hukumomin Jihar babbar manuniya ce da ke nuna kwanakin jam’iyyar kidayyu ne a kan gadon mulki. A kwanan nan kadai fitaccen dan kasuwa Alhaji Mustapha Asaija ya fita jam’iyyar da tsabar mutane 5, 000 tare da alkawalin tabbatar da nasarar PDP a Ambursa da kewaye tare da bayyana kasawar APC a mulki da rashin gani a kasa a matsayin dalilin fitarsu daga jam’iyyar.
“Babban kalubalen da Gwamna Atiku Bagudu ke fuskanta shi ne farin jini, karbuwa da goyon bayan da ya samu a 2015 yanzu babu shi domin yadda al’ummar mu suka yi tsammanin mulkinsa ya kasance ba haka ya kasance ba don haka Kabawa masu kishi da hangen nesa na jiran zaben 2019 domin su canza wannan Gwamnati daga sama har kasa bakidaya.” In ji Alhaji Umaru Technical (Wamban Yauri) a tattaunawarsa da LEADERSHIP A Yau Juma’a.
Ya ce “Matsalar da APC ke fuskanta a Kebbi shine rashin aiwatar da muhimman ayyukan raya jiha da ci-gaban al’umma a cikin Birnin Jiha da Kananan Hukumomi 21 wadanda za a iya tallatawa tare da nunawa jama’a a matsayin ci-gaban da Gwamnatin Jihar ta samar.”
Babban dan siyasar ya kara da cewar matsala ta biyu ita ce jama’a sun dawo daga rakiyar mulkin jam’iyyar APC wadda suke kuka da salon mulkin ta a jiya kuma suke ci-gaba da kokawa a yau saboda gasawa jama’a aya a tafin hannu a mulkin ta wanda ya haifar da fatara, talauci da karuwar rashin ayyukan yi da tabarbarewar tsaro da na tattalin arziki.
Wakilinmu ya labarto cewar fitowar Dan Takarar Gwamnan Kebbi na PDP daga Yankin Kabi ta Arewa a Masarautar Argungu babbar dama ce da za ta taimakawa jam’iyyar kwarai ainun domin yankin babban yanki ne wanda ke da tasiri a siyasar Kebbi, amma kuma bai taba samun ci-gaban yin Gwamna ba a bakidaya tarihin jihar don haka al’ummar yankin suna cike da farin ciki tare da kwakkwaran shirin zaben yi wa kai ta hanyar zaben Sanata Isa Galaudu a matsayin sabon Gwamna.
Baya ga Sanata Isa Galaudu da ya zama babbar barazana ga PDP a Kebbi haka ma ya tsayar da gogaggen kuma fitaccen dan siyasa wanda ya yi fice wajen taimakawa al’umma Abubakar Malam (Shettiman Gwandu) ya taimaka wajen canza lissafin siyasar jihar ta yadda a yanzu haka wasu na cewa ‘yan APC suna bacci ne da ido daya.
Shettiman Gwandu babban jigon dan siyasa ne wanda ya taba zama Dan Takarar Gwamnan Kebbi a jam’iyyar DPP a 2007 da CPC a 2011, hasalima Kotun Daukaka Kara A Sakkwato ta soke zaben Gwamna Sa’idu Dakingari a kan kalubalantar zaben da ya yi tare da umurtar sake sabon zabe. Haka ma a 2015 shi ne ya yi wa jam’iyyar PDP takarar Sanata a Mazabar Kabi ta Tsakiya.
Tsohon Mataimakin Kuntorola- Janar na Hukumar Kwastam, karbabben dan kasuwa kuma babban manomi Shettiman Gwandu daga babbar Masarautar Gwandu ya fito mazaba daya ne da Gwamna Bagudu don haka a bayyane yake cewar kai tsaye zai raba kuri’un Kabi ta Tsakiya yankin da Gwamnan ke bugun gaba da shi a inda aka fito tare da shakku a yau a bisa ga yadda jama’a suka juya masa baya.
A ra’ayinsa Hassan Haruna Shayau daga Birnin Kebbi ya bayyana cewar “Duk wanda ya kwana ya tashi a Kabi ya san APC ta shiga cikin rudani a bisa ga karbuwa da goyon bayan da PDP ke samu a kowace rana. La’akari da matsalar rashin bunkasa Jihar Kebbi, yaudarar manoma da shirin bunkasa aikin gona da bayar da rance, matsalolin ‘yan fansho wadanda ke bin Gwamnati bashin sama da naira biliyan daya, rashin tsayar da ‘yan takarar da jama’a ke ra’ayi duka matsaloli ne da za su sa PDP ta fadi zabin 2019.” Ya bayyana.
Shi kuwa Alhaji Ibrahim Manzo Argungu cewa ya yi “Babu wata jam’iyya a kowace jiha a Nijeriya da ta tsayar da ‘yan takara masu matukar karfi da tasiri ga jama’a irin PDP a Kebbi. Sanata Isa Galaudu kowa ya san ba kyalle ba ne a fagen siyasa babban bargo ne wanda ya samarwa kansa suna wajen share hawayen al’umma. Haka ma abin farin ciki ne yadda Shettiman Gwandu ya aminta da zama Mataimakin Galaudu duk da cewar ya yi ta neman kujerar Gwamma wanda hakan kadai ya nuna dan siyasa ne mai kishin Jihar Kebbi da zuciya daya wanda ya fifita son ci-gaban jama’a fiye da komai.” In ji shi.
To amma a bangarensa Faruku Aliyu ya bayyana cewar maganar PDP ta samu nasara a kan jam’iyyar APC zance ne kawai na siyasa domin Kabawa sun yadda da jagorancin da Gwamna Bagudu ke yi masu na aiwatar da mulki nagari don haka shine zabin su a 2019.
Shi kuwa Hassan Jega cewa ya yi “Ko kadan ba na shakkun Gwamna Atiku Bagudu zai sake lashe zabe a karo na biyu domin APC SAK za a yi kamar yadda aka yi a 2015 don haka tun da Buhari ne dan takara to ba mu da matsala a Kebbi don cikin ruwan sanyi za mu yi wa PDP a kaye a ko’ina.” Ya bayyana.
Hon. Sha’aban Maga Zuru na da ra’ayin a zaben 2019 babu wata maganar yin ‘Sak’ domin ‘yan Nijeriya sun gano kuskuren da suka yi na zaben APC da dukkanin ‘yan takarar ta a 2015. “Idan har ‘yan APC na tunanin za a yi Buhari SAK a 2019 to sun yi kuskure domin Atiku Abubakar ne za a zaba domin talakawa sun jiya a jikin su. Haka ma a yanzu lokaci ne da jam’iyyar PDP za ta kafa mulki a Kebbi musamman a bisa la’akari da gagarumar karbuwar da jam’iyyar da ‘yan takarar ta suka samu a lungu da sakon jihar.” In ji shi.
Hon. Sha’aban wanda ya fito daga Masarautar Zuru ya bayyana cewar yana da tabbacin Gwamnatin Sanata Galaudu/Shettima za ta zama Gwamnati mafi amfani da alfanu ga al’umma wadda za ta bada fifiko wajen kawar da matsololin al’umma da inganta jin dadin su domin ko ba komai ‘yan siyasa ne wadanda a jiya da yau suka san ciki da wajen matsalolin jama’a da sanin hanyoyin magance su.
Da aka tambaye shi ko ya ya mulkinsa zai kasance idan aka rantsar da shi a matsayin Gwamnan Kebbi a Mayun 2019, Sanata Isa Galaudu ya bayyana cewar zai gudanar da shugabancin gaskiya a tafarkin gaskiya, bunkasa jihar da al’ummar ta tare da shimfida ayyukan da za su yi tasiri a rayuwar talakawa da al’umma bakidaya kamar yadda ya bayyana a wajen kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa a Birnin Kebbi.
“Idan aka zabe ni a matsayin Gwamna na yi alkawalin farfadowa da tattalin arziki, da inganta sha’anin ilimi, magance matsalar rashin aikin yi da ke addabar matasa, bunkasa aikin Gwamnati, biyan kudaden fansho da garatuti kan kari tare da fitowa da ingantaccen shirin bunkasa aikin gona na zahiri tare da rance mai sauki ga manoma tare da mayar da Jihar Kebbi a abin koyi da kwatance.” Ya bayyana.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!