Connect with us

RAHOTANNI

2019: Ina Da Karfin Gwiwar Cin Zabe – Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana fatan da yake da shi na sake cinye zaben 2019 da za a yi, inda ya tabbatar da cewa; “nasara ta mu ce.” Inji shi.
Shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne a lokacin wani zaman tattaunawa da kwamitin kamfen dinsa wato PCC wanda ya gudana a fadar gwamnati dake birnin tarayya Abuja. Ya roki membobin kwamitin da su jajirce tare da sadaukarwa bisa aikin da aka dora musu.
Shugaban kasa ya kara da cewa; “Ina mai rokon ku da ku nuna jajircewa da sadaukarwa bisa aikin da aka dora muku. Bamu da wata tantama cewa nasara tamu ce; kuma tabbas namu ne. amma wannan ba ya nufin mu koma mu runtsa ba ko da dan lokaci ne.”
Buhari ya ci gaba da cewa; “Duk da muna fatan cewa mu ne zamu yi nasarar zaben, amma ina mai shawartarku da yin aiki tukuru domin tabbatar da nasararmu.” Har wala yau shugaban kasa ya ce; “Ina mai shawartarku da ku fuskanci kalubalen dake gaban ku da wanda ‘yan Nijeriya za su fuskance ku da shi, ina da fatan akan ku cewa tabbas zaku cimma nasara.” Inji shi.
Har wala yau shugaban kasar ya shawarci membobin kwamitin da su gudanar da kamfe mai tsafta tare da tabbatar da nasarar jam’iyyarsu da ‘yan takararsu.
“Ba sai na fada ba, amma zabinku ba abu ne mai sauki ba, domin a lokacin samar da wannan kwamitin, a karshe jam’iyyar ta samu wadanda suka dace. Kune hasken jam’iyyarnan, ina mai tabbatar muku idan har ku ka zama masu hadin kai, tare da kusantar da juna da tafiya tare, to ina mai tabbatar muku da cewa; babu wani dan adawa da ba za ku yi nasara akansa ba.” Ya jaddada.
A karshe, Buhari ya ce; manufar zaman kwamitin shi ne domin tabbatar da tsare-tsare kwamitin domin gudanar da Kamfe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!