Connect with us

NAZARI

Gudummowar Ma’aikatar Yada Labarai Ga Samun Nasarar Gwamnatin Ganduje

Published

on

Idan dai ana bukatar samun nasara a kowace Gwamnatin ya zama wajibi a aje kowane abu a gurbinsa, yin hakan ke haifar da da mai ido ta fuskar samun nasarar aikace-aikacen Gwamnati.
A Jihar Kano babu shakka yana daga cikin musabbabin Nasarar Gwamnatin Ganduje samar da nagartaccen shugaba a ma’akatar yada labarai ta Jihar Kano.
Masu fashin bakin harkokin cigaban al’amuran yau da kullum sunyi ittifakin cewar ma’aikatar yada Labaran Jihar Kano bata taba yin dacen shugaba kamar wannan lokacin da gogaggen dan Jarida, masanin makamar aiki, kwararre a aikin yada labarai Malam Muhammad Garba wanda a halin yanzu ke jagorantar Ma’aikatar ba. Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya samu kyakkyawar nutsuwa ta fuskar kare muradun gwamnati da kyautata alaka da kafafen yada Labarai.
Babban abinda ya fi daukar hankalin jama’a shi ne yadda Kwamishinan ma’aikatar yada labaran Jihar Kano Malam Muhammad Garba ke aiki ba dare ba dara wajen fadakar da al’ummar Kano birni da karkara ayyukan da gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ke aiwatarwa Kanawa. Wannan ya hada da gabatar da cikakken bayanin sakamakon zaman Majalisar zartasawa, wanda Jama’a aduk mako ke kasa kunnuwa domin jin sabbin ayyukan da Gwamnatin Ganduje ta amince a gudanar a fadin Jihar Kano.
A kwanakin bayan Jam’iyyun adawa sun kafawa Gwamnatin Kano Karkashin jagorancin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje karan tsana kan halin da wasu ke ta tseguntawa jama’a cewa daliban dake karatun akasashen wajen na cikin wani hali mara dadi. Wannan tasa Kwamishinan ma’aikatar yada Labaran na Jihar Kano Malam Muhammad Garba tare da shugaban hukumar ba da talalfin karatu ta JIhar Kano bis aumarnin gwamna Ganduje ya ci gaba da sanar da irin tagomashin da Gwamnati ke yiwa wadancan dalibai. Domin tuni gwamnatin Kano ta warware matsalar tulin basukan kudaden karatun da aka gadar mata, wanda a halin yanzu ta kara da tura mata 100 zuwa kasar Saudiyya domin karin karatu.
Duk wani al’amari da ya kamata jama’ar da ake mulka su sani a Jihar Kano komai a bayyana ake gudanar dashi, domin Malam Muhammad Garba ya tabbatar da samar da kyakkyawar danganta ka tsakanin Gwamnati da kafafen yada labarai, ta yadda a kod yaushe suke da wata tambaya ko karin haske kan wani aikin gwamnati kofar Malam Muhammad Garba a bude ta ke kuma kulluma lale marhabin yake idan an tunkare shi da neman karin bayani kan wasu aikace-aikacen gwmnatin Kano.
Malam Muhammad Garba kafin zamansa Kwashinan ma’aikatar yada labarai, al’adu, matasa da wasanni ya taba zama shugaban kungiyar ‘yan Jaridu na Jihar Kano, daga nan kuma ya shugabanci kungiyar a matakin kasa, inda daga nan ne kuma ya zama shugaban kungiyar a Africa baki daya, taka wadannan mukamai ya bashi damar fahimtar duk wata matsalar harkokin yada labarai da kuma hanyoyin warware su. Babu shakka ko hasidin iza hasada ya aminta da nagartar Malam Muhammad Garba.
Duk da kasancewar sa Dan Jarida wannan bai hana shi gudanar da kyakkyawar mu’amilla da ‘yan siyasa ba, musamman ganin lokaci ne na siyasa kuma ita ake a halin yanzu, ya zama zakaran gwajin dafi tsakanin takwarorinsa, domin shi ne kwamishinan da akullum yake fadi tashi da ‘yan jam’iyya domin kare kimar Gwamna da Gwamnatin Kano.
Malam Muhammad Garba ne kwamishinan da Ma’akatar ta taba yi wanda aka tabbatar da ya dawo da kimar aikin harkokin yada labarai a fadin Jihar Kano.
Alokacin wannan gwamnati ne aka sake farfado da kamfanin Jaridar nan ta Triumph wadda ita ke sahun aba wajen ya ye duk wani gogaggen dan Jarida a Kasar nan, wannan Kamfani ya zama kufai a baya kasancewar an yi masa kisan mummuke. Amma zuwan wannan Gwamnati tare da kyawawan shawarwarin kwamishina Malam Muhammad Garba yanzu Kamfanin Triumph yake dawo tare da ci gaba da buga jaridun nan guda hudu wadda babu wata Jarida a kasarnan dake irin wannan gagarumin aikin.
Sanin hali da nagartar Malam Muhamamda Garba ya sa ahalin yanzu Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada shi shugaban kwamiitn yada labaran yakin neman zamensa a shekara ta 2019, Gwamna Ganduje ne ya bayyana haka alokacin da yake rantsar da sabbin kwamishinoni hudu da gwamnan ya gudanar a cikin makon nan a dakin taron na Coronation dake fadar Gwamnatin Kano. Wanann ba karamar farar dabara Gwamna Ganduje ya yi ba, domin hakan zai taimaka wajen wayar da kan al’umma Jihar kan kyawawan ayyukan da wannan gwamnati ta aiwatar a cikin shekaru uku da doriya.
Malam Muhammad Garba a lokuta daban daban shi ne ke zaman allurar dinke duk barata da ake ganin na kokarin tasowa, musamman yadda jam’iyyun adawa ke ta shaci fadi kan wasu al’amaru marasa tushe balle makama, amma dai jama’ar Kano shaida ne wannan jarumin namiji ya rungumi tsare tsaren tabbatar da samun nasarar Gwamnatain Ganduje a zabe mai zuwa. Domin shi ne kwamishina da ako da yaushe matukar yana gari zaka iske shi a ofishinsa yana ci gaba da karbar jama’a tare da
gudanar da ayyukan da aka dora masa nauyinsu.
Zuwan Malam Muhammad Garba wannan Ma’aikata ya sake farfado da kyakkyawan kokarin ma’aikatan wannan hukuma, kamar yadda aka sani ma’aikata ce dake kunshe da jajirtattun mutane masu dadadden tarihin nagarta ta fuskar aiki, samun ire iren wadannan ma’aikata ne ya taimakawa Kwamishinan samun nasarar da ake ta bayani akanta. Yanzu haka Ma’aikatar yada labaran Jihar Kano ke zaman madubi a tsakanin ma’aikatun da hukumomin Gwamnatin Kano, wannan kuma ya samu ne
sakamakon bayar da dama ga kowane ma’aikaci domin samun natsuwar gudanar da ayyukansa cikin kwanciyar hankali ba tare hantara ko tsangwama ba.
Yanzu da ake tunkarar zaben shekara ta 2019 ma’akatar yada labara ice ke sahun gaba wadda al’umma birni da karkara suka dogara da ita wajen jin duk wani motsin alhairi da gwamnati ke aiwatarwa, don haka ne ma kwamishina Malam Muhamamd Garba ke kara zaburar da kafafen gidajen radio da talbiji da jaridu domin tsayawa kan aikin su bilhakki da gaskiya, domin kamar yadda ya sha fada sune hanyar da al’umma ke sauararo domin jin halin da gwamnati ke ciki da kuma sakon da ake aikawa al’ummar karkara da birane.
Sai da kuma alokuta da dama Malam Muhammad Garba kan yi gargadi kan yada jita jita ko labarin kanzon kurege, yace yana daga cikin kwarewa a aikin jarida tabbatar da nagartar labari kafin fitar dashi ga al’umma, haka kuma ya kan ja kunnen manema labarai wajen kare mutuncin
aikin domin kaucewa zubar da darajar da aikin ke da ita. Yin kwakkwaran bincike kafin fitar da labarai ke tabbatar da nagartar kowane dan Jarida kuma shi ne abinda kullum Gwamnatin Ganduje ke
bukata, ya sha fadin cewa muna lale marhabin da duk wani tsokaci da zai sa wanann Gwamnati kara himma wajen ci gaba da kwararawa Kano da Kanawa ayyukan alhairi domin shi ne abinda ke zuciyar Gwamna Ganduje da duk mai kaunar wannan Gwamnati.
Samar da nagartattun wakilan gwamnati wanda aka damkawa amanar rike wani bangare na gwamnati shi ne ke kara haska kyakkyawar makoma dakuma nasarorin Gwamnati, a Jiha irin ta Kano samar da mutanen kirki masu kishin cigaban Jihar ne zai karawa Jama’ar Jihar himma wajen sake zabar wannan gwamnati, yana daga cikin dalilan nada kowane kwamishina domin taya gwamna rike jama’a da taimakonsu kamar yadda aka tabbatar wannan Kwamishina Malama Muhammad Garba na fatar da Gwamna Ganduje kunya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!