Connect with us

MANYAN LABARAI

INEC Ta Bayyana Matakai Bakwai Da Mai Zabe Zai Bi

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta ayyana wadansu matakai 7 da mai zabe zai bi a lokacin zaben da zai gudana a wata mai kamawa.
Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na Intanet, inda ta jero su daki-daki duk da ba ta canza wani abu daga matakan da aka sani ba a zabukan da suka gabata.
Matakan kamar yadda INEC din ta jero sune kamar haka:
Mataki na 1: Da isarka rumfar zabe, ka bi layi, sannan sai ka gabatar da kanka ga jami’an INEC din da ka tarar wato (APO111) a rumfar zaben, wanda sune za su tantanceka su tabbatar maka da cewa ko a nan zaka yi zabenka ko ba a nan ba. Sannan sune za su duba hotonka dake cikin katin zabenka na dindindin su ga ko kai ne a jiki. Idan har kai ne ko ke ce a jiki, za su nusasshe ka zuwa ga wani jami’in INEC din (APO1).
Mataki 2: Jami’an INEC din (APO1) za su bukaci ganin katin zabenka na dindindin domin tabbatar da sahihancinsa tare da duba bayanan dake jikinsa ta hanyar amfani da na’urar zabe. Ko shi ko ita, za su bukaci da ka sa hannunka a na’urar domin tabbatar da cewa katin zaben na ka ne, inda nan take na’urar zaben zai nuna suna, hoto, da kuma hoton yatsun hannun duk wanda ya yi rijista a wannan rumfar zaben.
Mataki 3: Daga nan kuma sai a sake tura ka wurin wani jami’in (APO11), wanda shi ne zai bukaci da ka ba shi katin zabenka domin tabbatar da sunanka da bayaninka a cikin takardar rijistar zabe. Za a sakawa sunanka maki, sannan a maida maka da katin zabenka. Daga nan shi ko ita za su saka maka alama a hannunka domin ka gudanar da wannan zaben. Idan ko har ba a samu sunanka a cikin rijistar masu zabe ba, ba za a barka ka yi zabe ba.
Mataki 4: A nan Jami’in dake kula da wannan rumfar zabe PO, zai buga hatiminsa tare da saka hannu, da kuma tabbatar da kwanan wata a jikin takardar zaben. PO zai nade takardar ya mika maka. Daga nan zai nuna maka ko zata nuna maka wurin da aka tanada domin ka je ka gudanar da zabenka, inda a nan ne zaka yi zaben cikin sirri.
Mataki 5: Dan yatsan da ka ba da aka saka maka alama a yatsan, da shi zaka yi amfani wajen zaban dan takarar da kake so ta hanyar dangwalawa a wurin da aka samar domin dangwalawa dan takarar da kake so. Daga nan sai ka nade takardar zaben kamar yadda PO ya baka.
Mataki 6: Bayan ka yi zaben, zaka ajiye takardar zaben a cikin akwatin da aka tanada a gaban jama’ar da suke rumfar zaben. Sannan sai ka bar wurin da ka dangwala kuri’arka.
Mataki 7: Daga nan sai ka bar rumfar zaben, ko ka jira idan ka so hakan. Amma zaka kasance cikin natsuwa ba tare da tada hatsaniya ba, har ka jira lokacin da za a ayyana wanda ya ci zaben a wannan rumfar zaben. Sannan za a manna sakamakon zaben a kowanne rumfar zabe domin mutane su ga wane ne ya ci zaben a wannan rumfar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!