Connect with us

WASANNI

Mourinho Yana Farin Cikin Koma Wa Real Madrid

Published

on

Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da Chelsea, Jose Mourinho ya bayyana cewa abin farin cikine ace ana dangan taka da kungiyar daka taba rikewa kuma yana fatan hakan anan gaba.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ce dai ta kori Mourinho a watan daya gabata sakamakon rashin tabuka abin arziki da kungiyar takeyi kuma yana rikici da wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar.
Tun bayan barinsa Manchester United, kungiyoyi da dama dai sun nemi Mourinho mai shekara 55 ciki har da tsohuwar kungiyarsa ta Benfica, wadda ya koyar tun yana matashin mai koyarwa a kasarsa ta haihuwa Portugal.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai tana fatan ganin ta dauki mai koyarwa na din-din-din sakamakon mai koyar da ‘yan wasan kungiyar na yanzu, Santiago Solari rikon kwarya yake rikewa kuma an tunanin shugabannin kungiyar zasu nemi Mourinho domin yakoma a karo na biyu.
“Abin farin cikine ace tsohuwar kungiyar daka taba rikewa tanason ka sake komawa tabbas ina farin ciki da haka saboda haka naji lokacin da nakoma Chelsea” in ji Mourinho wanda ya taba koyar da kungiyar Inter Millan ta kasar Italiya.
Mourinho dai ya shafe shekaru uku a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid daga shekara ta 2010 zuwa ta 2013 inda a tsakanin shekarun ya lashe kofin laliga guda daya da kuma gasar cin kofin Copa Del Rey.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!