Connect with us

WASANNI

Pepe Ya Koma Tsohuwar Kungiyarsa Ta Porto

Published

on

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da F/C Porto wanda ya shafe shekaru yana buga wasa a kungiyoyin kwallon kafa da dama ya koma tsoguwar kungiyarsa data fara haska shi har duniya ta sanshi.
Wannan dan wasan dan asalin kasar Portugal ba kowa bane illa Pepe, inda a yanzu ya koma kungiyar kwallon kafa ta f/c Porto bayan kungiyarsa ta Basiktas ta kasar Turkiyya ta sallameshi daga buga mata wasa.
Pepe dai ya bugawa kungiyar FC Porto wasanni har na tsawon shekaru 3 a baya daga shekara ta 2004 zuwa 2007, inda ya buga musu wasanni 64 yaci kwallaye guda 6 kafin yakoma Real Madrid
A shekara ta 2007 ne ya koma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid inda ya kwashe shekaru 10 a kungiyar, ya buga musu wasanni 229 sannan yaci kwallaye guda 13 sannan ya lashe manyan kofuna daga ciki akwai gasar zakaru ta nahiyar turai guda 3.
A shekara ta 2017 ne ya koma kungiyar kwallon kafa ta Basiktas, inda suma ya buga musu wasanni 33 yaci kwallaye guda 3 sai dai a yanzu haka ta tabbata cewa ungulu ta koma gidanta na tsamiya tunda Pepe ya koma tsohuwar kungiyarsa ta F/c Porto dake kasarsa ta haihuwa wato Portugal.
Pepe ya bugawa kasarsa ta haihuwa wato Portugal wasanni 103 yaci kwallaye guda 7 sannan yana daya daga cikin ‘yan swasan da suka wakilci kasar a shekara ta 2016 da suka lashe kofin nahiyar turai a kasar Faransa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!