Connect with us

LABARAI

Egbetokun Ya Zama Sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas

Published

on

An maye gurbin Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Legas wato Imohimi Edgal da sabon Kwamishina mai suna Kayode Egbetokun, wanda kafin zaman shi a matsayin Kwamishinan jihar, shi ne mataimakin Kwamishinan da aka maye gurbi.

Edgal, an nada shi a matsayin Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Legas a ranar 30 ga watan Agustan 2017, yanzu haka an maishe shi sashen lura da bama-bamai a Hedikwatar ‘yan Sandan dake Abuja.

Sabon Kwamishinan ‘yan Sandan, wato Egbetokun an haife shi ne a ranar 4 ga watan Satumban 1964 a Erinja dake karamar hukumar Yewa ta Kudu a jihar Ogun. Inda ya shiga aikin Dan Sanda a ranar 3 ga watan Maris din 1990 a matsayin mataimakin Sufiritanda na ‘yan Sanda.

Sannan a shekarar 1999, aka nada shi a matsayin babban mai kula da tsaron gwamnan jihar Legas, wato Sanata Bola Tinubu. Sannan ya rike muka mai daban-daban, wanda ya hada da Kwamandan sashen masu kawo agajin gaggawa ta hukumar ‘yan Sanda a jihar Legas, Kwamandan ‘yan Sandan kwantar ta tarzona a garin Benin, Babban Jami’i mai kula da bangaren zambo a birnin tarayya Abuja da dai sauran su.

Ya kammala digirinsa na farko  ne a shekarar 1987, inda ya karanci lissafi daga Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Legas (UNILAG). Daga nan ne ya fara karantar da darasin lissafi a Kwalejin Fasaha ta Yaba dake Legas din. Daga baya kuma ya shiga aikin dan Sanda.

Har wala yau ya yi digirinsa na biyu a bangaren Injiniya a jami’ar UNILAG, sannan ya yi babbar difloma a bangaren Tattalin Man Fetur daga Jami’ar Delta dake Abraka, sai kuma ya sake yin wata digiri na biyu a bangaren kasuwanci daga Jihar Legas dake Ojo.

Kafin nada shi a matsayin Kwamishina a halin yanzu, Egbetokun shi ne mataimakin Kwamandan Kwalejin ‘yan Sandan Nijeriya dake Ikeja a jihar Legas.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!