Connect with us

LABARAI

Mutum 3 Sun Rasa Rayukansu A Sabon Hari A Jihar Kaduna

Published

on

Akalla mutane 3 ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da wadansu mahara suka kai a daren jiya Lahadi a tsakanin Asso da gadar Tanda dake karkashin Masarautar Gwong a karamar hukumar Jema’a a jihar Kaduna.

Peter Averik, Ciyaman din karamar hukumar, ya tabbatar da faruwar kai harin a yau Litinin. Inda ya ci gaba da cewa; an kai harin ne da misalin karfe 7:30 na dare, a yayin da wadansu mahara da ba a tantance ko su wane ne ba suka bude wuta akan mutanen da ba su ji ba su gani ba a yayin da mutanen ke tafiya a tsakanin Asso da gadar Tanda. Ya kara da cewa; “An fada min cewa maharan an gan su kawai sun fara harbin mutane ne a daidai gadar, inda ake tunanin sun harbi mutanen ne domin ka da su tona musu asiri.”

Ciyaman din ya ce; Mutum daya ya mutu a nan take ne, a yayin da mutane 2 da suka raunata, sai aka kai su asibitin Fadan Kagoma, inda daya daga cikinsu ya mutu da safiyarnan, sakamakon mummunan raunin da ya ji. Averik ya tabbatar da cewa; mutum na ukun da ya samu rauni, an samu gawarsa daga baya a yau Litinin a wani daji a daidai kauyen Wazo kafin a isa Aso.

Sai dai ya ce; an gama shirye-shiryen kai wadanda suka samu rauni zuwa asibitin Barau Diko dake Kaduna, bayan asibitin Sir Patrick Memorial Hospital dake Kafanchan ta nemi a yi hakan. Ciyaman din ya tabbatar da cewa; tuni aka kai jami’an tsaro wuraren da aka kai wannan harin, domin ganin an tabbatar da tsaro a yankin. Ya kuma ce; gwamanati zata tabbatar ta kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Idan ba ku manta ba, rahotanni sun tabbatar da cewa; mutane 15 ne a kwanakin nan suka rasa rayukansu a yayin da 17 suka samu rauni a wani hari da wadansu mahara suka kai ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a Unguwan Pa’ah dake kauyen Gwandara dake Masarautar Godogodo dake karamar hukumar Jema’a.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!