Connect with us

LABARAI

An Kaddamar Da Tashar Ruwa Ta Farko A Arewacin Najeriya

Published

on

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da tashar sauke dakon kayan jiragen ruwa ta farko a Arewacin Najeriya, wacce a ka yi wa lakabi da Baro Inland Water Port, a jihar Neja a ranar Asabar 19 ga Janairu, 2019.
Tun asali an bayar da kwangilar aikin gina tashar ruwan ne a zamanin tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, tsakanin shekarun 2011 zuwa 2012 a kan kudi Naira biliyan Shida, amma sai a ka yi watsi da aikin ba a iya aiwatar da shi ba.
Zuwan Buhari a matsayin shugaban kasa a shekara ta 2015 ne a ka dawo da cigaba da aikin, don kammala shi. Kamfanin CGCC Global Project Nigeria Limited ne su ka gudanar da kwangilar aikin.
Janar Manaja mai kula da Corporate Affairs na hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa, Mista Tayo Fadile, ya ce, an saka wa sabuwar tashar ruwan isassun kayan aiki da ofisoshin da a ke bukata, don gudanar da harkokin gudanarwa da na mulki.
“An kuma saka hasken lantarki wanda ya kai karfin 100KBA,” in ji shi, ya na mai kara wa da cewa, “tashar ruwa ta Baro na daya daga cikin tashoshin ruwan da gwamnatin tarayya ta gina ne domin taimaka wa aikin yasar Kogin Neja.”
“A na sa rai Tashar Baro za ta samar guraben aiki guda 2,000 na ma’aikatan da za a dauka kai-tsaye, sannan kuma an kiyasat cewa tashar za ta samar da aikin yi ga dubunnan daruruwan mutane.
“Tashar za ta kuma taimaka wajen rage yawan zirga-zirgar manyan motocin dakon kaya, wanda hakan zai kara wa manyan titinan kasar nan karko kafin su fara lalacewa,” a cewarsa.
Ya kuma ce, hukumar tasa ta fara aikin yashe matafiyun ruwa, wadanda su ka hadu da tashar da kuma fadada su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!