Connect with us

MAKALAR YAU

Shiga Siyasa: Abin Da Zai Samu ’Yan Fim Idan Aka Canza Gwamnati (II)

Published

on

Kamar yadda kowa ya sani yanzu harkar Fim ta zama abin da ta zama saboda wadanda suke yin ta da gaskiya sun gano wata hanyar mai sauki bullewa saboda suna ganin bata lokaci ne ka tsaya kana wani shutin din fim da wata kila asara kawai za ta tafka.
Yanzu sai dan siyasa sai ya baki ko ya baka ko kuma ya baku kudin da sai ku yi shekara ba ku same su saboda sun gano amfaninku a wajan jama’a amma da zaran sun gama da ku shikenan wai makadi ya fada wuta! wasu za a nema, an fi yi wa ‘yan mata haka amma su mawaka ana dadewa kafin a watsar da su.
A satin ya gabata na yi alkawarin irin abubuwan da za su sami ‘yan Fim musamman wadanda suka yi hijira daga harkar Fim zuwa harkar siyasa, irin wanda idan wasa ya baci ba su san yadda za su fitar da kansu ba balanta wani na tare da su.
Zan dan koma baya in duba tarihi sannan in dawo wannan lokaci da muke ciki domin rarrabe aya da tsakuwa a tsakanin wadanda mutane, domin ko ba komi ya kamata ace harkar fim tana da tunani game da abin da ya shafi siyasa da ‘yan siyasa, ko ba komi ance jiya ake karantawa a gane yau.
Ba laifi bane idan mutun ya ce ga ra’ayinsa, musamman abin da ya shafi siyasa amma nasa’ar da kake yi ne ka dauke katsokam ka mika wajan wani, da babu tabbas lallai ka nuna rashin sanin zaman duniya da kuma rayuwa.
Lokacin da harka Fim ta fada cikin wani irin mawuyacin hali sakamakon badalar Maryam Hiyana, da yawan jama’a musamman wadanda ba Kano suke da zama ba sun tausayawa ‘yan Fim da harkar Fim baki daya.
Suma a bangaran ‘yan fim din sai da suka kusa rasa uwar da ta haifesu saboda yadda aka yi amfani da siyasa ta hanyar ‘yan siyasa aka gasa masu aya a hannu, amma wannan bai isa yasa su halkalta ba.
Baki dayan maganata zan takaitata ne a jihar Kano kafin in tsallaka zuwa wasu jahohi da kuma tarayyar Najeriya baki daya. Babu wanda yake fatan abubuwan da suka farua harkar fim tarihi ya maimaita kansa, amma idan ba a yi hankali ba abin da zai zo nan gaba yana iya fin na baya. Allah dai Ya sawake.
A sakamakon fadawar ‘yan Fim a hannun Malam Rabo wanda ‘yan siyasa ne suka yi amfani da wannan damar bayan sun gama cin amfaninsu, daga karshe dole tasa suka yanke shawarar goya ma tsohon gwamna Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bayan domin dai a samu a fita daga wancan kangin da suka kira na zalunci da danniya.
Goyan bayan da suka nunawa gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya taimaka masa wajan samun nasara shi kuma duk da cewar babu wani abin a zo gani da ya yi wa harkar fim amma dai ‘yan fim na jin dadi da suka fita wancan ukubar zuwa rayuwa irin ta masu ‘yanci.
A wancan lokacin duk da cewar suna kallon an zalunce su ba su nuna zakewa so sai ba wajan yin adawa, fata dai kawai shi ne a fita daga hannun Malam Rabo shugaban hukumar tace finafinai ta jihar Kano kuma daga karshe an fita.
Sai da ya zama kusan duk ‘yan fim sun zama masoyan gwamna Rabi’u Musa Kwankwanso. Wannan ina magana ne akan ‘yan fim baki daya, kafin ‘yan bani na iya su zama uwa makarbiya a harkar shiga siyasa ina magana ne akan mawakan yanzu.
Sannan lokacin da gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ta fadi akwai ‘yan fim din da suka nuna biyayya da da’a a gareta amma daga karshe sun koma kamar mujiya a cikin tsintsaye, ga su nan dai ba wani farin jini ba jari babu daukakar kamar suna yawo gantali.
Kuma duk da ba fada ba, suma ‘yan fim din da suka bi gwamnati a wancan lokacin sun yi nadamar yin abin da suka yi na bijirewa ‘yan uwansu da suke ganin an zalunce su amma ana ganin a’a sune dai suka ki bin umarnin gwamnati ko kuma bara mata baya a wancan lokacin.
To yanzu dai kowa ya ga yadda wasa ya baci tsakanin ‘yan fim da kuma mawaka da suka goyi bayan gwamna Rabi’u Musa Kwankwanso a wancan lokacin yanzu kuma sun samu wanda ya fi shi saboda sun raba gari da shi inda har ta kai ana yi masa zanbo da cin fuska a wakokin siyasa.
Kuma abin mamaki mutanen da suka ce tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwanso ya yi masu abin kirkir ya yi rawar gani inda ya kwace su daga hannu Malam Rabo, yanzu saboda dalilin siyasa an koma cin mutuncin juna.
Wani abin da yasa da yawan jama’a ke ganin wautar ‘yan Fim musamman wadanda ke Kano a yanzu shi ne irin yadda salon siyasa yake neman canzawa wanda idan ba sa lura ba kuma aka sa hankali da kuma hangen nisa, to nan da wasu makwanni labarin na iya canzawa.
Abin da ake nufi anan yanzu ba yanke hukunci nake yi ba, amma tambayar anan shi ne idan Allah ya ba dan takarar da gwamna Rabi’u Musa Kwankwanso ya tsaida nasara a zabe mai zuwa menene makomar ‘yan fim a jihar Kano? Kar mu manta su ‘yan fim kamar jami’an tsaro ko ‘yan jarida suke.
Ya kamata ne ace kowa na su ne, domin dai babu inda ba su da masoya kuma ko shaidan ya zama shugaba dole suna da rawar da za su taka a matsayin su na masu sana’ar yi da suka ragewa gwamnatin nauyi ba dan karami ba.
Mutane irin su Rarara da Nazifi Asnanic da suka yi wa gwamna Rabi’u Musa Kwankwanso wakokin soyayya da yabo a wancan lokaci yanzu kuma sun dawo suna tsine masa, ina za su sa kansu idan dan takarar shi ya yi nasara, ko ko ana nufin sai kawai mu ji wakokin taya murna daga wajan su.
Haka jama’a da dama sun dauka cewa Rarara zai dauki darasi daga abin da ya faru akan idonsa na cin fuska da yin shagubai ga tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim shekarau saboda sun raba gari da Shugaba Muhammadu Buhari kwatsam saboda dalilin siyasa sai gashi sun sake haduwa a tafiyar shugaba Buharin tare da su acikin inuwa daya, kuma kwanan nan ake sa ran cewa Buharin da kansa zai daga hannun Shekarau ya ce a zabe shi a jihar Kano.
Don Allah wa gari ya waya yanzu? Ko ko yanzu mu jira ranar da Buharin zai zo Kano zamu ji sabuwar wakar da Rarara ya yi wa Shekarau ya wanke shi daga wancan cin fuska da cin mutunci da ya yi masa. Wannan ina bada misali ne da shi saboda shi zuwa ya yi Kano.
Idan muka koma akan Nazifi wanda shi dan Kano babu inda ya fi masa garin haihuwarsa, yanzu idan dan takarar gwamna jihar Kano a karkashin jam’iyyar adawa ya samu nasara wane darasi zai koya; ’yan fim da mawakan da suka kware masa baya a lokacin da yake bukatar mutane?
Bahaushe ya ce da muguwar rawa gara kin tashi, yanzu da ‘yan fim da mawaka da ace sun rike kimarsu da sana’rsu da masoyansu na gaskiya da yanzu sun fi haka domin babu wata ranar da za a ce an daina yin wannan sana’a to amma saboda irin yadda ‘yan fim da mawaka suka tsoma wannan harka cikin matsalar da ba a san ranar fita ba, hakan yana jefa shakku akan dorewar sana’ar a jihar Kano idan aka samun canjin gwamnati.
Hatta ita wannan matsalar ta nuna wane muke so, ba ma son wane, ta yi matukar tasiri a tsakanin ‘yan fim masu goyan bayan bangaran gwamnati da kuma wadanda suke neman mulki inda yanzu ta kai ana yi wa juna kallon hadarin kaji maimakon su dauki dabi’ar nan ta siyasa ba da gaba ba.
A mako na gaba zan kawo wasu misalai akan masu fitowa a finafinai da suka dauki matsaya cewa su wane suke so basa son wane, to idan wanen nan da kuke ki ya samu nasara ya ke nan. Ali Nuhu ya taba gaya mani wata magana da ya ce tunda yake a duniya babu wani mutun da ya taba yi masa kyautar da wani gwamnan jam’iyyar PDP a yanzu ya yi masa, to amma yau ya nuna cewa shi APC yake yi.
Sai dai kuma Ali Nuhu yana cikin mutanen da a yanzu suka rufe idonsu wajan maida al’amuransu katsokam akan harkokin siyasa a maimakon harkar Fim wanda yake ita ce gaskiya. Zan ci gaba Insha’Allahu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!