Connect with us

RAHOTANNI

Ba Za Mu Amince Da Duk Wani Nau’in Magudin Zabe Ba — Mai Rakumi

Published

on

Hadaddiyar kungiyar ’yan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin jam’iyyun hamayya sun yi zargin cewa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufai yana kokarin amfani da wadansu masu kula da al’amuran tsaro ta yadda zai samu yin magudin zabe a zaben shekarar 2019 mai zuwa a duk fadin Jihar, wanda kuma suka ce ba za su amince da haka ba.
Wannan zargi yana kunshe ne a cikin wata takarda da aka karanta wa manema labarai lokacin da hadaddiyar kungiyar ta yi taron manema labarai a cibiyarsu da ke Kaduna a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2019.
Jagoran kungiyar ta CUPP, Hon. Umar Ibrahim Mai Rakumi ya shaida wa manema labaran cewa suna kira tare da jan hankalin daukacin jama’a, musamman Jami’an tsaron ‘yan Sanda, Hukumar zabe mai zaman kanta da dukkan Hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki a kan irin kokarin da Gwamna Malam Nasiru Ahmed El- Rufa’i yake yi.
Saboda haka ne ma kungiyar ke jawo hankali da cewa “don haka ne ma muke fadakar da daukacin Jama’a da dukkan wadanda abin ya shafa cewa dauke jami’an ’yan sanda da ake kokarin yi a wannan lokaci da zabe ke kara karatowa ba daidai ba ne, saboda karara lamarin na bayar da wata manufa ce ta daban, musamman neman da Gwamnan ke yi na manyan Hukumomi na Gwamnatin tarayya su amince da Jami’an tsarin-sa kai da ake kira “Kato da Gora” domin su zama daga masu aikin kula da tsaro a zanen Mai zuwa. Wannan ba daidai ba ne, kuma ba za mu amince da shi ba.”
Haka kuma kungiyar ta yi zargin cewa a Gwamnan na da hadamar ganin ya ci gaba da zama a kan kujerar mulkin Jihar, ya kuma kaddamar da wadansu sababbin ’yan kula da harkar tsaro masu suna “Kaduna state Local Gobernment Safety and Emergency Management Bolunteers”, da za a yi amfani da su a matsayin masu bayar da tsaro a akwatunan zabe Ko rumfunan zabe.
Ta ce hakika babu wanda zai amince da wannan, domin tsarin ba karbabbe ba ne. “Saboda haka muna jan hankalin Hukumar zabe, Hukumomin tsaro, ‘yan Nijeriya da kuma jami’an kasashen duniya masu sa idanu a harkokin zabe, tare da zaben baki daya game da wannan matsalar da za ta haifar da rashin lafiya a harkar siyasa.
Ya ci gaba da cewa wannan tsarin da Gwamnan ke kokarin kawo wa ya Saba da tsarin tanade-tanaden da Hukumar zabe ta ke da shi domin yin zaben 2019 mai zuwa. Dukkan Jam’iyyun siyasa na da alhakin ganin an yi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana kamar yadda aka saba yi.”
Daga nan sai ta ce, “kungiyar CUPP na da cikakken tabbacin cewa rundunar ’yan Sanda da kuma dukkan jami’an Hukumomin Gwamnatin tarayya za su iya bayar da ingantaccen tsaro, a yi shi cikin kwanciyar hankali da lumana a dukkan tashoshin jefa kuri’ar da ake kira akwatunan zabe inda jama’a za su jefa kuri’unsu.”
“Don haka muna kira ga Hukumomin jami’an tsaro baki daya da kuma Hukumar zabe su tabbatar tsarin gudanar da zabe da zaben kansa a babban zaben shekarar 2019, ba wai kawai ingancin zaben ba, har ma Sai ya zama abu ne karbabbe da zai cika dukkan sharuddan kasa da duniya baki daya,” in ji Kungiyar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!