Connect with us

LABARAI

Saraki Ga ‘Yan Nijeriya: Kar Ku Bari A Yi Muku Magudi A Zabe Mai Zuwa

Published

on

Shugaban Majalisar Dattawa, kuma babban daraktan Kungiyar kamfen din dan takaran Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Dakta Abubakar Bukola Saraki, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da suka mallaki katin su na jefa kuri’a a duk kasar nan, da su tabbatar da sun fito sun kada kuri’a a ranar 16 ga watan Fabrairu, 2019.
Cikin sanarwar da mai ba shi shawara na musamman a kan harkokin manema labarai, Yusuph Olaniyonu, Saraki, ya bayar da dalilai masu yawa a kan yanda ya zama tilas ga ‘yan Nijeriya da su fito baki-dayansu su shiga cikin zaben da ke tafe, ya yi nuni da cewa, matukar mutane suka fito da yawa, ba ta yanda za a iya murguda sakamakon zaben.
“Duk mun ga abin da ya faru a cikin shekaru hudu da suka gabata. Lokaci ya yi ga ‘yan Nijeriya da su fito su zabi bunkasan tattalin arziki a kan talauci; su zabi samar da tsaro a bisa yanda rashin tsaro yake ta kara yaduwa; su zabi shugaban da ya cancanta a kan shugaban da zamaninsa ya shige.
“Lokaci ya yi da duk ‘yan Nijeriya za su fito su zabi shugabannin da suka san abin da suke yi, Atiku Abubakar, Peter Obi, na Jam’iyyar PDP, a matsayin shugabannin su, wadanda suka yi alkawarin gyara Nijeriya, kuma a shirye suke da su dawo da martabar Nijeriya,” in ji Saraki.
“Kirana ga matasan kasarmu, ina son ku sani, bai kamata ku rika komawa baya-baya ba. A duk Duniya, matasa kamar ku ne suke zaban ma kansu shugabannin da za su jagorance su. Matasan Nijeriya su ma sun sami irin wannan daman a halin yanzun.
“Na karanta maganganu masu yawa a kan matasan, inda suke cewa ba za su yi zabe ba, domin ko sunyi zaben ba shi da ma’ana, domin an ce masu za a yi magudi ne a zaben. In kun fito da yawa ku ka yi zaben ba za su iya yin magudi din ba!” ai yawan wadanda ba su fito sun yi zaben ne ba masu magudin za su yi amfani da shi su yi magudin.
“Ina son ku dauki wannan zaben da mahimmanci, in mun hada kanmu za mu kafa tarihin ceton Nijeriya.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!