Connect with us

SIYASA

Zabe: APC Ce Za Ta Yi Nasara A Sahihin Zabe –Oshiomole

Published

on

Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomole ya tabbatar da cewa; idan har aka gudanar da sahihin zabe a kasarnan, to APC ce zata lashe zaben.

A sanarwar da Malam Lanre Issa-Onilu, Sakataren watsa labaran t APC din na kasa ya fitar, ya tabbatar da hakan ne a wani zama da kwamitin zartarwa  na jam’iyyar ya gudanar a garin Abuja.

Issa-Onilu ya ce; zaman a wannan lokacin ya zama wajibi ne domin yin duba da shirye-shiryen zaben da ke gabatowa wanda zai gudana a ranar 16 ga watan Fabarairun nan.

Ya ci ga da cewa; Oshiomhole shi ne ya jagoranci zaman, inda kuma zaman ya samu halartar Jagororin jam’iyyar na jihar, ‘yan takarar Gwamna a jam’iyyar da kuma Sakatarorin jam’iyyar na duk fadin kasarnan.

Oshiomhole  ya tabbatar da cewa; idan har aka gudanar da sahihin zabe, to tabbas jam’iyyar  ce zata lashe zaben.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: