Connect with us

LABARAI

Zaben 2019: Dukkan ’Yan Takara Namu Ne, In Ji Sarkin Kano Sanusi

Published

on

Zaben 2019: Dukkan ’Yan Takara Namu Ne, In Ji Sarkin Kano Sanusi

Daga Nasir S. Gwangwazo

 

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa, dukkan ’yan takara a kowacce jam’iyya na fadarsa ne, saboda kasancewar masarauta a matsayin uwa kuma uba ga dukkan ’yan siyasar Najeriya.

Sarki Sanusi II ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya kai ma sa ziyara a fadarsa da ke birnin Kano a yayin gudanar ya je jihar, domin gudanar gudanar da yakin neman zabe.

A ta bakin mai martabar ya ce, “duk alakar wannan gida ta mutuntawa ga wadannan ’yan takara, mu na nan a matsayinmu na iyayen al’umma. Ko me ya taso wajenmu za a zo. Don haka kowa namu ne.”

Mai martaba Sarkin ya kuma yi kira ga jama’a da su fito su amshi katin zabensu, wanda za a rufe karba a yau Litinin, ya na mai cewa, “mu na kira ga jama’a da su fito su karbi katinsu na zabe, don su samu damar zaben wadanda su ke so.”

Daga na sai ya yi fatan za a gudanar da zabe cikin lisilama. “Kuma mu na fatan za a gudanar da zabe cikin lumana,” in ji shi.

Sarkin ya bayyana farin cikinsa da ziyara da dan takarar ya kawo tare da tawagarsa, inda ya ce, “Mu na yiwa mai girma Wazirin Adamawa da Mai girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ’yan tawagarsu maraba da zuwa, kuma mu na fatan su yi taro lafiya. Allah ya ba mu lafiya da zama lafiya.”

A nasa jawabin, Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar, ya bayyana wa Sarkin cewa, sun zo fadar tasa ne, domin neman tubarrakinsa a matsayinsa na uba ga kowa tare da sanar da shi abinda ya kawo shi kasarsa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!