Connect with us

WASANNI

Cavani Bazai Buga Wasan PSG Da United Ba

Published

on

Watakika dan wasan gaba, Edinson Cabani ba zai buga wa kungiyarsa ta Paris St-Germain gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League da Manchester United ba sakamakon ciwo dayaji a ranar Asabar.
Dan wasan mai shekara 31 ya yi rauni ne a bayan da ya ci fenariti a fafatawar da Paris St-Germain ta yi nasarar doke Bordeau 1-0 a ranar Asabar kuma bayan rashi daga wasan kociyan kungiyar ya tabbatar da cewa dan wasan yaji ciwo.
Daman tun frako dan wasan Brazil, Neymar ba zai buga fafatawar gida da waje da PSG da Manchester United za su yi ba, sakamakon jinya da ya ke yi wanda kuma ba karamar matsala kungiyar tasamu a daidai wannan lokacin
Neymar ya yi rauni ne a ranar 23 ga watan Janairu a wasan da PSG ta doke Strasbourg a Kofin kaluba na FA, bayan da likitoci suka duba shi ne suka sanar da zai yi jinyar mako 10 kuma tuni kungiyar ta fitar darai dawowarsa.
“Tabbas Cabani yaji ciwo wanda mummunan labari ne muka samu waboda haka bashi da tabbacin samun damar buga wannan wasa da zamu fafata a yau’ in ji kociyan kungiyar ta PSG, Thomas Tuchel.
Yaci gaba da cewa “Munyi rashin Neymar yanzu kuma mun sake yin rashin Cabani wannan ba abu bane mai dadi saboda haka dole sai ‘yan wasan da muke dasu sun sake dagewa domin maye gurbin wadancan ‘yan wasan da muka rasa”
Kawo yanzu Kylian Mbappe ne ke koshin lafiya cikin ‘yan wasan gaba da ke ci wa PSG kwallaye a fitattun da take da su sai kuma tsohon dan wasan Manchester United din wato Angel Di Maria.
PSG za ta ziyarci filin wasa na Old Trafford domin buga wasan farko a yau Talata 12 ga wannan watan na Fabrairu, sannan su buga wasa na biyu a ranar 6 ga watan Maris a Faransa wanda shima Neymar bazai buga ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: