Connect with us

LABARAI

Hukumar Kashe Gobara Ta Ceto Mutum 147 A Shekarar 2018 A Abuja

Published

on

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara na Abuja, Mista Jerry Timbeh, ya bayyana cewa hukumarsa ta ceto yarukan mutum 147 da kuma dukiyoyi wanda kudinsu ya kai naira miliyan 2.3 daga lamarin gobara, tun daga watan Junairu zuwa watan Disamba ta shekarar 2018. Timbeh ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa ranar Lahadi a garin Abuja. Ya kara da cewa, an samu nasarar ceto rayukan mutum 17 a cikin wata uku, yayin da aka ceto rayukan mutum 16 a cikin wata shida, an ceto rayukan mutum 50 a cikin wata tara, sannan kuma an samu nasarar ceto rayukan mutum 64 a cikin karshen shekarar.
Da yake bayar da bayanin kayayyakin da aka mai do, ya bayyana cewa kayayyakin da aka ceto cikin watan Disamba sun fi yawa a shekarar, yayin da na cikin watan Maris su ne mafi kankanta. Timbeh ya kara da cewa, hukumar ta samu kiran waya a kan lamarin gobara kusan sau 440, guda 47 daga mazauna garin Abuja. Ya kuma bayyana irin saraukar da kai da kuma jajircewan da jami’an da ke dakin iko suka yi wajen amsa kiran waya tare da daukar mataki nan take.
Kamfanin dillanci labarai na kasa ta ruwaito cewa, yankunan da lamarin gobaran ya fi kamari a cikin garin Abujan su ne, kubwa, Asokoro da kuma Gwarimpa.
Jami’in hulda da jama’an ya yi kira ga mazauna garin Abuja su yi kokarin kiyaye muhallinsu a kan duk wani aiki da zai janyo musu gobarar tare da zai janyo musu asarar rayuka da kuma na dukiyoyi. Ya kuma shawarci mazaunan su tun ga kokarin kiran hukumar da wuri idan aka samu lamarin gobarar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!