Connect with us

LABARAI

Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Karar Jam’iyyar APC Ta Jihar Ribas

Published

on

Kotun Kolin kasarnan ta yi watsi da karar da jam’iyyar APC rashen jihar Ribas ta daukaka a gabanta game da zabukan 2019.

Wani kwamiti ne mai Alkalai biyar karkashin jagorancin Olabode Rhodes-Vivour ya yi watsi da karar da wani bangare na APC karkashin jagorancin Rotimi Amaechi ya shigar.

Bangaren Amaechi sun shigar da karar ne suna kalubalantar hukuncin da babbar kotun jihar ta zartar na hana jam’iyyar gudanar da zaben fitar da gwanayen da za su yi wa jam’iyyar takara a zabe mai zuwa.

Wannan hukuncin ya biyo bayan hukuncin kotun daukaka kara ta Nijeriya ne da ya tabbatar da wani hukuncin na babbar kotun jihar ta Ribas wanda ya soke zaben fitar da gwani da wani tsagin jam’iyyar ya gudanar.

Babbar kotun ta yanke hukuncin ne bisa karar da bangaren Sanata Magnus Abe suka shigar tun da farko wadda ta hana yin zaben fitar da gwanayen.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!