Connect with us

KIWON LAFIYA

Likitoci Sun Shawarci Majinyata Da Su Dinga Shan Ruwa Sosai  

Published

on

Wani babban likita, Dakta Roland Aigbovo na babban asibitin Asokoro dake garin Abuja, ya shawarci majinyata da su dinga shan ruwa sosai, musamman a wannan lokacin da ake gab da shiga zafi a birnin tarayya Abuja, likitan ya bada wannan shawarin ne a yayin da yake ganawa da manema labarai yau Talata a garin Abuja.

Ya bayyana cewa ruwa yana da matukar amfani a jikin mutum, musamman da yake ruwan yana kunshe da wasu sinadarai wadanda jikin dan adam yake matukar bukatar su, in kuwa mutum ya rasa su a jikin shi akwai yiwuwa ya shiga matsalar rashin ruwa a jiki.

Ya kara bayyana cewa shan ruwa zai yi matukar kara wa jikin mutum lafiya, sannan zai kare shi daga fadawa wasu cutukka na daban, misali rashin shan ruwa sosai yana iya wahalar da kodar dan adam, har zai iya kaiwa ga haifar da ciwon kai mai tsanani, sannan cin abinci mai kyau ma yana matukar taimakon lafiyar jikin dan adam, musamman ma ganye da ‘ya’yan itatuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!