SHARHI
Uwar Marayu Ta Dauki Nauyin Biya Wa Marayu Kudin Makaranta A Kano

Hajiya Halima wadda aka fi sani da Uwar Marayu ta bayyana aniyarta ta biyawa Marayun da kuma dinka masu kayan makaranta ga duk Marayan da aka shigarshi makarantar Abubakar Sadik Islamiyya daka Kawon mai gari a Karamar Hukumar Nasarawa, Jihar Kano. Hajiya Halima Uwar Marayau ta bayyana haka ne alokacin bikin saukar Karatun Dalibai goma da makarantar ta gudanar ranar Lahadin data gabata. Hajiya Halima ta cigaba da cewa yin hakan ya zama wajibi domin muhimmancin tallafawa marayu da kuma tabbatar da ganin suma sun samu damar karatu kamar kowa.
Taron saukar karatun wanda shi ne karo biyar an gudanar dashi a harabar makarantar dake Kawon Mai Gari Layin Baba dashi, Tun farar Safiya Dalibai da iyayen yara suka yiwa harabar makarantar tsinke domin shaida wannan taro wanda jama’a suka jima suna kwadayin zuwansa, wannan kuma baya rasa nasaba da irin salon saukar karatun daliban wannan makaranta wanda ba duk makaranta ke irinsa ba, kasancewar sai an jinjina karatun dalibai kafin amincewa da shiga cikin jerin wandanda za’a yiwa bikin saukar Karatun.
Da yake gabatar da Jawabinsa Shugaban Makarantar Malam Abubakar Sadik ya bayyana farin cikin bisa yadda Allah ya ara mana numfashin ganin zagayowr wannan lokaci, yace muna kara godiya ga Dagacin Kawo Alhaji Kabiru bisa irin gudunmawar da yake baiwa duk wata sabgar harkokin addini da kuma zaman lafiyar al’ummar da yake shugabanta, haka kuma Abubakar Sadik ya iinjinawa kokarin malaman makarantar bisa sadaukarwa da suke nunawa alokacin dawainiya da daliban makarantar.
Malam Abubakar Sadik ya nuna damuwarsa bisa irin rikon saikanar kashin da masu rike da madafun iko ke yiwa harkokin makarnatun islamaiyyu, yace ba zamu manta da irin gudunamawar da Kiristoci suka yiwa wannan makaranta abaya ba, inda suka bayar da sorayen gidajensu domin ci gaba da koyar da ‘ya’yan Musulmi karatun addini, wanda hakan ko kadan abin kunyane ga shugabannin mu musamman gwamnatocinmu. Don haka sai ya jinjinawa kokarin da wani dankishin kasa da al’ummata ya yiwa wannan makaranta wajen gina wannan makaranta, yace yanzu haka babbar matsalar da muke fuskanta itace rashin gyaran wasu daga cikin ajujuwan da har yanzu muka kasa karasa aikinsu domin fara karatun dalibai acikinsu, don haka muke kira ga masu fatan dibar garabasa ranar gobe alkiyama dasu yi kokarin duba halin da makarantar ke ciki domin bada tasu gudunmawar.
Alhaji Ubale Kawo mataimakin na musamman ga Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci a rubuto bukatun makarantar domin gabatarwa Gwamnati domin ganin abinda zata iya aiwatarwa, sannan kuma ya bukaci mahalarta taton da kowa ya bayar da gudunmarwasa domin cigaban wannan makaranta. Alhaji Ubale Kawo ya yi tsokaci kan wasu abubauwa da ya kamata iyaye su mayar da hamkali musamman lura da tarbiyyar ‘ya’yansu domin ganin an smau nagracciyar al’umma.
Ana sa Jawabin Dagaci Kawo wanda dansa Malam Nura Kabiru Kawo ya wakilta ya bayyana bukatar da ake da ita na ganin ana tallafawa irin wadanan Makaratu, sannan kuma jadadda farin cikinsa bisa kokarin shugaban Wannan makaranta Malam Abubakar Sadik bisa yadda yake Dawainiya wajen ilimantar da’ya’yan al’ummar wannan yanki. Don haka sai ya bukaci jama’a dasu ci gaba da zama lafiya sannan kuma ya bukaci iyaye su lura da yaransu alokutan zabuka masu zuwa domin kaucewa shiga hayaniyar siyasa, a karshe Malam Nura ya gabatar da sakon karramawar da Dagacin Kawo ya yiwa shugaban Makarantar Malam Abubakar Sadik.
Cikin wadanda suka gabatar da jawabai a wurin bikin saukar karatun akwai wakilin kungiyar tallafawa harkokin makabartu, ‘yan takarkarun Jam’iyyar PRP da ADP, da sauran manyan mutane ne suka halarci taron saukar karatun.
-
HANTSI1 day ago
Atiku Barazanar APC
-
RAHOTANNI1 day ago
Ba Mu Da Masaniyar Cafke Wani Da Sakamakon Zabe Na Bogi A Abia, Cewar ‘Yan Sanda
-
MANYAN LABARAI2 days ago
Dage Zabe: Ka Da Mu Karaya Akwai Fata –Saraki Ga Al’ummar Nijeriya
-
BUDADDIYAR WASIKA1 day ago
Baba Buhari, Mu Na Murna Da Tazarce
-
LABARAI2 days ago
Gwamnati Ta Ba Da Umurnin Sake Bude Kan Iyakokin Kasa
-
LABARAI2 days ago
Dage Zabe: Ba Karamin Mamaki Abun Ya Bani Ba –Atiku
-
MANYAN LABARAI1 day ago
Ko A Dage Zabe Ko Kada A Dage Sai Mun Kayar Da Buhari, In Ji Kera
-
KASASHEN WAJE9 hours ago
Mayakan Boko Haram 187 Sun Ajje Makamai A Kamaru