Connect with us

MAKALAR YAU

Zaben Gwamna: Da Gaske Sanata Yakubu Lado Ya Sayar Da Takararsa?

Published

on

Maganar da a yanzu ta fi kowace daukar hankali da tashe kai harda farashi a siyasar jihar Katsina ita ce wanda ke cin kasuwa a kafafen sadarwa na soshiyal midiya wato dai maganar sayar da takarar Sanata Yakubu Lado dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP
Wannan magana dai har gobe babu wanda zai gaya maka inda ta samo asali sai dai irin abin nan da ake cewa kura sunanki ya baci tun kina karama, ma’ana dai sanin asali ya sa kare cin alli.
Idan akwai wani batu da yanzu haka ya tsayewa Sanata Yakubu Lado Dan marke da sauran wadanda suka tsaya a jam’iyyar PDP domin ganin abinda zai turewa buzu nadi to wannan batu na daga cikin sahun gaba, wanda ko shakka babu akwai alamun yanka bayan da yarfen siyasa.
Duk wannan fadi tashin yakin neman zaben da aka gudanar fiye da watanni biyu wannan magana bata ta so ba, kuma babu wanda ya yi ta ko da sunan yakin neman zabe amma yanzu abin ko maganar nasarar shugaba Buhari ba ta kai wannan batu na sayar da takarar Lado ba.
Abin tambaya shin daman yana sai da takara ko ko yanzu ne zai fara? Sannan idan an tashin sayarwa wane dan takara ne zai saya? Kuma wanene zai shiga tsakani domin ganin wannan ciniki ya tabbata? Sannan ma nawa ne zai saida wannan takara ta shi da aka ce ya ware mata naira biliyan shida cas.
Idan babu amsar wadannan tambayoyin gaskiya akwai lauje cikin nadi akan wannan makarkashiya da aka shiryawa Sanata Yakubu Lado Dan Marke wanda na yi imanin cewa wannan hayagaga da ake yi masa inda zai samu wanda zai saye da tuni ya tullar da mangwaro ya huta da kuda.
Ana fasasa Lado da wani namijin duniya wanda haka ke nuna shakku game da sai dai wannan takara ta shi, har ma wani lokaci ana yi masa kirarri da canza su Lado, idan dai wannan kirari da gaske ne a ni a tawa fahimtar ba zai saida takarar shi ba sai ma dai a nemi alfarma ya yi.
Sannan idan aka yi waiwaye adon tafiya, lokacin da jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina ta tsayar da Sanata Yakubu Lado a matsayin wanda zai yi mata takara a wannan zabe maganaganu da yawa sun rika fitowa tun wancan lokacin inda wasu ke cewa kamar PDP bata shirya shiga zabe mai zuwa ba wasu kuma na ganin akwai yadda aka yi wai an dafa kaza an ba mai ita kai.
Daga cikin ‘yan takara guda tara da suka nuna sha’awarsu ta tsayawa wannan takara dukansu babu wanda bai fi Lado cancanta ba inji wasu, sai dai ana ganin yanzu yanayin zabe ya canza babu yadda za a ci zabe ba tare da kudi ba, daga nan aka fara tunanin wanene zai fito da kudin da za ayi yakin neman zabe har a samu nasara?
Wannan da ma wasu dalilai sun sa wasu na ganin Lado kadai zai iya fitowa da kudi a yi wasan mutuwa ala bishi duk abinda zai faru ya faru saboda baya da wata tuhuma da ake yi masa a matakin jiha ko gwamnatin tarayya sumul kalau yake. (fresh)
Kamar yadda na ce akwai masu cewa tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema ne ya kawo Lado saboda wani dalili wanda aka ce wata yarjejeniya ce wai tsakaninsa da gwamnatin jihar Katsina idan ya tsayar da Lado da an yi zabe zai fadi shikenan shi kuma sannu a hankali maganar shari’arsa zata shiririce.
Wasu sun so su gasgata wannan batu a daidai lokacin shugaban jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina Honorabul Salisu Yusuf Majigiri ya zama wanda zai yi wa Sanata Yakubu Lado mataimaki a karkashin jam’iyyar PDP duk da cewa shi ne shugaban jam’iyyar kuma gashi mai ajiye mukamin sa ba.
Har ma akwai wani lokacin da mataimakin shugabban jam’iyyar APC na shiyyar Funtua Alhaji Bala Abu Musawa ya kalubanci Honorabul Majigirin da ya ajiye mukaminsa na shugaban jam’iyyar sannan a cigaba da fafatawa da shi a yakin maganganun siyasa domin acewar Bala Abu ba su san da wa suke magana ba da dan takarar mataimakin gwamna ko ko da shugaban jam’iyyi?
Jama’a da dama na ganin cewa kamar akwai kamshin gaskiya akan wannan batu domin idan babu rami mai ya kawa maganar rami? Honorabul Majigiri dai ya yi shiru bai taba cewa ufan ba game da wannan tirka-tirka ta rika mukamai guda biyu.
Sai dai duk da haka wasu sun rika yaba masa akan cewa idan da ba shi ne shugaban jam’iyyar PDP a jihar Katsina ba to yanzu anyi sadakar shekara ukun ke nan da mutuwarta an yaba masa so sai akan namijin kokarin da ya yi na rike jam’iyyar wanda daga karshe aka yi zabe bata da kujera ko daya.
Kadda in cika ku da surutu bari in koma akan batun da nake na maganar sayar da takarar Lado wanda yanzu duk wanda zaka tambaya zai gaya maka cewa shima ya ji maganar ko dai a bakin jama’a ko kuma a kafar sadarwa ta yanar gizo sai ba babu wanda zai iya gaya maka wanda za a saida mawa.
Kuma kamar yadda na ce wannan magana ta fara ne gab da za ayi zaben shugaban kasa, amma ta fi cika gari da ko’ina bayan kammala zaben shugaban kasa, wasu na son su ce gwamna Masari aka saidawa ko kuma za a saida mawa amma suna jin tsoro saboda babu wata hujja a zahiri.
Sannan yadda alama ta nuna cewa jam’iyyar APC ta yi nasara a dukkanin kujerun Sanatotci da ‘yan majalisar wakilai to ga mai hankali babu bukatar ace wai gwamna Masari zai tsaya yana maganar sayan takara da shi, abinda kawai yake jira yanzu shi ne lokaci, nan da kwana uku jama’a su cika masa alkawarin da suka dauka na zabensa.
To, idan wannan magana ta zama gaskiya to abin ya zama biyu ke nan, wannan maganar ta sayar da takarar Lado wani sabon salon bugun jeka ka mutu ne da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC suka bullo da shi domin karya gwiwar Lado da jama’arsa saboda a zahira babu maganar sannan kullin ita ce abin tattaunawa tsakanin matasa kai har da manya.
Kazalika wani abu da ke nuna cewa babu wancan maganar ta sayar da takara illa dai kawai ana neman a fusata Sanata Yakubu Lado ne ya ce ya fasa takarar shi ne a jiya wasu gungun ‘yan ‘yan jam’iyyar PDP na halas wadanda suke tsoron zuwa lahira a tambayesu me yasa suka bar PDP sun yi wani gangami a gidan gwamnatin jihar Katsina inda suka nuna cewa su ‘yan PDP ne kuma ba su bar PDP ba amma kuma ba za su zabi wanda jam’’iyya ta tsaida masu ba saboda rashin cancantarsa.
Sannan magana da ake yanzu ita ce, duk wani wanda aka san yana taimakawa tafiyar Lado a bangaran sadarwa na zamani wato soshiyal Midiya tsohon gogarman PDP Bature Umar Masari ya kwashesu dukka ya maido su tafiyar gwamna Masari wanda muna iya cewa saboda an ga Lado baya da wadanda za su kare shin a kafar sadarwa shi yasa ake yi masa yarfe da cewa ya saida takararsa alhali ko gobe idan ka tambaye shi zai gaya maka cewa shi ne zai cinye zaben da za a yi a ranar asabar mai zuwa.
Wannan fa shi ne a bugeka kuma a hanaka kuka, ba a sayi takarar tasa ba, sannnan ana yi masa rubdugu da cewa ya sayar bayan an raba shi da wadanda za su kare shi tare da yin bayani game da takararsa, ni dai har yanzu ban ji daga bakin Lado cewa maganar takararsa ta na nan ba, abinda kawai na sani shi ne har yanzu bai sai dai ba.
Yanzu idan ta tabbata cewa Lado bai saida wannan takara ta shi ba, aka yi zabe bai samu nasara ba, zai tabbatar da maganar da ake cewa zai koma jihar Kano inda daman can yake zaune ya cigaba da harkokinsa sai wani lokacin ya zo wani sabon salon wanda ba a sani ba ko ko zai cigaba da gwagwarmayar siyasa har sai abinda lamba ta nuna?
Daga yau laraba zuwa jibi juma’a wadannan maganganu za su tabbata idan kuma ya yi nasarar saidawa, to ina tabbatarwa jama’a cewa sai an samu wasu sun dawo wajansa bayan sun guje shi bisa dalilin wai ya kwace motocin yakin neman zabensa tun kafin a yi zaben. Allah shi ne masani da fatan za ayi zabe lafiya a gama lafiya
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!