Connect with us

SIYASA

’Yan Adawa Na Yada Labaran Karya Ne Don Cin Ma Burin Siyasarsu –Hon. Balarabe

Published

on

Kasa da awanni kafin zaben ‘yan majalisar dokokin jiha da na gwamna, rahotanni sun karade kafafen sadarwa na zamani inda ake yayata cewar hukumar da yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa ( EFCC) ta cafke wasu muhimman mutane da ke da kusanci da gwamnatin jiha. Wanda hakan ya jawo hankalin mutane da rashin ganin kimar rahoton wanda ya sanya ‘yan jarida mayar da hankali akan wannan labarin.
Hon. Ibrahim Balarabe, kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na daga cikin wadanda ake yada wannan labarin kanzon kuregen akan su.
A tattaunarwarsa da manema labarai bayan ya kada kuri’arsa a mazabar mai katifa da ke cikin garin Kagara, ya ce maganar kame ba gaskiya ba ne, tun lokacin da ake maganar ma shi ya dawo gida don huskantar zabe kuma gaya kowa ya gan shi kuma ku din gaya kun ganni a mazaba ta har na jefa kuri’a ta, don haka irin wadannan labarai ba sabbin abu ba ne ai, kawai masu yin shi suna yi ne kawai don batanci da cin ma burin siyasar su.
Yanzu ka ganarwa idanun ka irin abinda PDP ke yi nan, yanzu ga mutanen nan sama da ashirin da tanbarin PDP a wuyansu duk kansu nan wai jami’an PDP ne. Ina aka taba tura mutane masu yawa haka a mazaba daya sunan sanya ido a runfar zabe daya.
To mu ba shi ne a gaban mu ba, saboda gwamnatin jiha ta yadda da kanta ba ta aminta a matsantawa jama’a ba wai don samun nasarar zabe, muna da yakinin cewar mutanen da suka zabe mu a 2015 su din ne idan sun gamsu da irin rawar ganin da maigirma gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello cikin shekaru uku zuwa hudun nan zasu sake ba shi damar karin wa’adin shekaru hudu a gaba, don haka idan dan hamayya ya yi abinda yake yi yanzu ba zai hana Allah ya yi ikonsa akan wanda ya yi niyyar baiwa damar hawa kujerar ba.
A matsayina na mai rike da kujerar kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na san irin ayyukan da maigirma ya yi a kananan hukumomi ashirin da biyar da ke jihar nan, don haka ire-iren wadannan karairayin ba sa karya mana guiwa suna kara mana azama ne na ci gaba da ayyukan raya kasa.
A baya jama’a sun saba akwai shi dukiyar gwamnati ana almubazaranci da su ba tare da la’akari da irin halin da kasa ke ciki ba, zuwan wannan gwamnatin ta dakile wadannan abubuwan, sanin kowa ne duk da tarnakin da gwamnati ta fuskanta lokacin da muka karbi mulki, mun samar da abubuwan more rayuwa ga al’ummomin mu, don haka gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello ba za tai kasa a guiwa ba, ayyukan da muka faro da yardar Allah zamu dora akan su idan mun dawo zango na biyu.
Ina jawo hankalin jama’ar jihar Neja da su ci gaba da baiwa gwamnati hadin kai wajen ganin an samu ingantacciyar zaman lafiya don ci gaban tattalin arzikin jihar mu da al’ummomin mu, APC jam’iyya ce ta talakawa, jam’iyya ce da ta zo da ingantattun muradun da za a yi alfahari da samuwarta.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!