Connect with us

KASUWANCI

Amurka Ta Rage Yawan Danyen Man Da Take Saye Daga Nijeriya Zuwa Kashi 43

Published

on

A bayanan kwanan da mahukunta a fannin sadarwa ta makamashi suka fitar ya nuna cewar, kasar Amurka ta rage yawan danyen man da take fitarwa daga Nijeriya zuwa gangunan miliyan 48.87 ko kashi 43 a 2018.
A shekarar data gabata daga sama da shekaru biyar na yawan danyen man da ya kai gangunan danyen mai miliyan 112.92 a 2017.
Bayanan EIA sun nuna cewar, kasar ta dauki gangunan danyen mai miliyan 75.81 a 2016, samada gangunan danyen mai 19.85 a 2015.
Fitar da danyen man da Amurka take yi daga Nijeriiya ya ragu da gangunan danyen mai 148.48 a 2012 zuwa gangunan danyen mai miliyan 87.40 a 2013.
Samfarin danyen mai Light sweet na Nijeriya yana yin kama da samfarin danyen light na Amurka.
Karin da aka samu na sarrafa danyen man Amurka, hakan ya janyo raguwar bukatar danyen mai na Nijeriya.
A 2014 farashin danyen mai a kasuwar duniya ya fara sauka akan ko wacce gangar danyen man dala 115, inda hakan ya sanya na Nijeriya ya ragu da Amurka take futarwa zuwa ganguna miliyan 21.24.
Acewar bayanan na EIA a karon farko, bayan shekarun da suka shude Amurka bata sayi danyen man daga Nijeriya ba cikin watannin Yuli, dana Agustan 2014 da kuma a cikin watan Yunin 2015 ba.
A 2010, Amurka ta sayi gangunan danyen miliyan 358.92 daga Nijeriya amma ta rage yawan jigilar sa zuwa ganguna miliyan 280.08 a 2011.
Acewar EIA, a bisa karin sarrafa danyen da Amurkk ta yi, fitar da man data yi ya kai bpd miliyan 1.9 a 2018, kimanin rubanya fitarwar data yi a 2017.
Danyen man da aka fitar daga Amurka zuwa Birtaniya ya wuce yawan da sauran kasashe suka fitar harda Nijeriyaa karo na farko tunda ta fara fitara a 2015.
A ranar Larabar data gabata, jaridar Financial Times ta ruwaito cewar, a Janairu, ta fitar da daidai da daya na ko wacce gangar mai daya a cikin ganguna hudu na matatun mai na Birtaniya ko kuma ganguna guda 264,000 a kulkum.
Har ila yau, a bisa bayanan da aka samo daga kamfanin Kpler sun nuna cewar, yawan danyen man na Amurka, yafi na kasashen Norway, Rusha, Nijeriya da kuma Algeria.
Kamfanin na Kpler ya kuma kasance wanda yake akan gaba wajen turwa Birtaniya danyen mai a shekarun da suka gabata.
Acewar EIA, Koriya ta Kudu ta shiga gaban China zuwa na biyu wajen turawa Amurka danyen mai baya ga Canada a 2018, ganin cewar kai mknbKoriya ta Kudu ya karu zuwa bpd 558,000 a Disambar
Amurka ta tura danyen mai na bpd 236,000 zuwa Koriya ta Kudu da kuma bpd 228,000 zuwa China a 2018.
Canada ta ci gaba da zamowa akan gaba a 2018, amma Koriya ta Kudu, ta na akan gaba a Disamba.
Amurka ta tura danyen mai na bpd guda 378,000 zuwa Canada a 2018, tare da wanda aka fitar a Disamba da ya kai yawan bpd 431,000.
Karin na danyen man Amurka ya auku ne saboda sarrafa bpd miliyan 12 da akayi zuwa sama daga bpd miliyan biyar.
Hakan ya sanya birnin Washington na Amurka bibiyar tsarin da gwamnatin shugaba Donald Trump ta samar akan habaka makamashin kasar, inda hakan ya sanya Amurka ta dara kasashen Rasha da Saudiyya a matsayin kasar da tafi ko wacce kasa a duniya sarrafa danyen mai da zamowa wadda tafi samar da iskar gas.
An kuma ci gaba da fitar da danyen mai bayan da Amurka ta cire takunkumin data kakabawa wasu kasashen larabawa tun a 1970 inda hakan ya sanya tattalin arzikin birnin Washington ya amfana musamman a fannin makamashi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!