Connect with us

KASUWANCI

An Samu Raguwar Masu Zuba Jari A Kasuwar Siyar Da Hannun Jari Ta Nijeriya

Published

on

A satin da ya wuce Kasuwar sayar da hannun jari ta Nijeriya taci karo da tasku, ayiyin da masu zuba jarin a kasuwar suka ragu
Amma a wancan satin na baya, Kasuwar ta samu ribar naira biliyan 36l, idan aka kwatanta da asarar naira biliyan 325 na satin da ya wuce da kuma raguwar masu zuba jari da kuma raguwar cinikayya da yawan kawa zuwa kashi 31.42 da kuma kashi 39.46.
Shiyar da aka sayar ta kai kashi 0.3, inda ta yi daidaito zuwa 32,049.73, inda ta kai kashi 1.57.
Har ila yau, kasuwar ta dan numfasa zuwa 0.65d ganin cewar an samu ribar 23
da kuma yin asara 37.
A cikin satin, Bankin Guaranty Trust Plc, Stanbic IBTC, Kamfanonin Holdings Plc, Nestlé Nigeria Plc da kuma Seplat Petroleum Debelopment Company Plc, sun fitar da sakamakon kudin su na 2018.
Masu fashin baki a Kamfanin Meristem Securities sun bayyana cewar, ayyukan da kamfanonin sukayi sunyi kokari kamar yadda sakamakon ya nuna hakan ya kuma sanya sun riba.
Bugu da kari, masu fashin bakin sun kuma yi nuni da cewar kammala zaben shugaban kasa da kwanan baya da aka kammala, ya rage fargabar dake cikin zuciyar masu zuba jarinsu a kasuwar.
Ganin cewar, saye da sayarwa a kasuwar kara zafafa a yayain da masu zuba jari a kasuwar suke ta fafutukar tsayawa da kafafansu saboda raguwar masu zuba jarin a kasuwar.
Bugu da kari, masu zuba jari a Kamfanin Betiba Capital Management sun bayyana cewar, cinikayya a kasuwar ta ci karo da nakasu saboda raguwar masu zuba jari a kasuwar da kuma a irin yanayin da kasuwar ta rufe a satin da ya gabata.
Kudin ruwa a fannin banki ya ragu a ranar Litinin data, inda na ASI ya karu da bps 95.
An kuma ci gaba da yin kokari a ranar Talatar data wuce, amma a matakin mai rauni ganin cewar Kasuwar ta haura zuwa samada bps 14.
Sai dai, a ranar Laraba tsegumi ya kara kunno kai a kasuwar akan kayan masana’antu da aka siyar da kuma mai fetur ds iskar gas, inda ASI ya rufe akan bps16.
Anci gaba da yin tsigumin har zuwa ranar Alhamis duk da cewar, sakamakon karshe na kudi da Bankin GTB ya fitar ya nuna cewar an samun karin kashi hudu.
Daga shekara zuwa shekara , an kuma samun karin kashi 10 na riba bayan an biya haraji da kuma samun ribar data kai kashi 7.3.
Masu zuba jari sun mayar da martanin akan hakan da kuma akan ribar fa aka fitar, amma basu ce komai akan bps na ASI ba.
Har ila yau, tsegumin ya gaza habaka yadda kasuwsr ta rufe a satin, ganin cewar kaya a kasuwar sunja da baya a ranar Juma’ar data gabata.
Sai dai, kuma ganin yadda kasuwsr ta rufe akan mataki mai kyau da aka fara cinta a satin, ASI a satin ya rufe akan samada bpd 31.
Fannin bankin ya samu ribar kashi 3.37, inda hakan ya sanya ya kara habaka ribar sa ta shekara zuwa shekara zuwa kashi 6.94.
Bankin Wema Plc ne ke akan gaba ga wadanda suka samu riba zuwa kashi 11.69, inda ya rufe akan kobo 86, inda Bankin Sterling Plc ke akan gaba na wadanda suka tabka asara.
Fannin kayan masana’antu ya ci gaba da samun nakasu ganin cewar asarar su ta kai kashi 0.98 kuma ribar su ta shekara-shekara ta kai 1.11.
Bayan sati hudu da suka wuce, tsegumin ya kara dawo kasuwar na tunanin masu zuba jari a fannin inshora ganin cewar ribar fannin ta ragu zuwa kashi 1.30 haka ribar fanin ta daga shekara zuwa shekara ta ragu zuwa kashi 3.53.
Fannin kayan masana’antu an samu ribar kashi 0.93 a cikin satin, inda hakan ya nuna fannin ya samu farafadowa daga asarar da akayi a satin da ya wuce, inda ribar ta daidaita zuwa kashi 3.12.
Fannin mai da iskar gas, sunci gaba da kare kambunsu a satin da ya wuce, inda suka samu kashi 2.56, inda Luma ribar daga shekara zuwa shekara ta kai kashi 3.44.
A sabin da ya gabata ba’a samu wadanda suka zamo zakaru a fannin mai da iskar gas ba, inda kamfanoni hudu na mai suka tabka asara,inda kamfanonin, Japaul Oil dana Maritime Serbices Plc suke akan gaba wajen yin asarar.
Amma ga saí daí Ana Hanuman kasuwar Zara fara da kafar dama a wannan satin bayan kawar kammala zaben na shugaban kasa da kuma tunanin samun karin masu zuba jari a kasuwar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!