Connect with us

LABARAI

Ganduje Ya Kara Bada Tabbacin Lashe Zaben Da Za A Maimaita A Kano

Published

on

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana farin cikinsa bisa yadda aka gudanar da zaben Gwamnan da ya gabata, Gwamna Ganduje ya tabbatarwa da al’ummar Kano cewa ya na karfin guiwar lashe zaben da za a sake gudanarwa ranar 23 ga watan March, 2019 wanda ake sa ran gudanarwa a wuraren da Hukumar Zabe mai zaman Kanta (INEC) ta
bayyana.
Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jinjinawa masu kada kuri’a bisa yadda suka yi fitar dango a ranar zaben, musamman yadda suka aminta da kadawa Jam’iyyar APC kuri’a, lallai mun tabbatar da cikakken goyon bayan al’ummar Kano ganin yadda dogwayen layuka suka cika akwatunan kada kuri’a, acewar Gwamna Ganduje.
Gwamnan na wannan jawabi ne jim kadan da dawowarsa daga babban birnin tarayya Abuja inda ya kai ziyarar kwana guda wanda daman haka yake cikin tsare tsarensa na ziyartar Abuja. Ya ce kamar yadda kowa ya sani Hukumar Zabe mai zaman Kanta (INEC) ta sanya ranar 23 ga watan Maris ya kasance ranar da za a sake zabe a wasu akwatunan zabe a Jihar Kano.
Saboda haka Gwamna Ganduje ya tabbatarwa Jama’a cewa da yardar Allah madaukakin Sarki Jam’iyyar APC zata samu gagarumar nasara a zaben da za a sake gudanarwa, don haka muna kara Godiya ga kowa da kowa tare da fatan za a gudanar da wannan zabe cikin kwanciyar hankali, kamar mai magana da yawun fadar Gwamnatin Kano Abba Anwar ya shaidawa Jaridar LEADERSHIP A Yau.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!