Connect with us

WASANNI

Manchester City Za Ta Iya Lashe Kofin Zakarun Turai

Published

on

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana cewa kungiyarsa za ta iya lashe kofin zakarun turai na wannan kakar inda ya bayyana cewa yanayin yadda suke buga wasa suke cin kwallo ne ya nuna hakan.
Manchester City ta caskara Schalke 04 daci 7-0 a karawa ta biyu ta Zakarun Turai ta tabbatar da wucewarta matakin dab da na kusa dana karshe a gasar ta zakarun turai wadda kungiyar take fatan lashewa a wannan kakar.
Dan wasan gaba na kungiyar, Sergio Aguero ne ya fara zura kwallo raga da bugun fanareti sannan ya kara ta biyu bayan minti uku, bayan da Raheem Sterling ya sa masa wata kwallo da dun duniya daga baya kuma Leroy Sane ya jefa ta uku sannan kuma ya bayar da kwallo har sau uku aka ci bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, lokacin da Manchester City ta shiga cin kwallo ba ji ba gani.
“Yana yin yadda muke buga wasa zai tabbatar da cewa ‘yan wasana sun shirya tun karar kowacce kungiya domin ganin mun samu nasara akanta saboda muna son lashe gasar ta bana’ in ji Guardiola
Dan wasa Raheem Sterling da Bernardo Silba da Phil Foden da kuma Gabriel Jesus dukkaninsu kowa ya ci kwallo , wanda a karshe Manchester City ta yi nasara da ci 10-2, jumulla gida da waje.
An fitar da Manchester City wadda ta farfado daga baya a karawarsu ta farko a Jamus ta yi nasara da ci 3-2, a wasan dab da na kusa da karshe a shekarar da ta wuce a haduwarsu da Liberpool, kuma ba ta taba cin kofin na Zakarun Turai ba.
A ranar Juma’a ne za a fitar da jadawalin wasan matakin na dab da na kusa dana karshe, na kungiyoyi takwas da karfe 11 na safe agogon GMT kuma za’a buga wasan karshe ne a kasar Sipaniya a filin wasa na Atletico Madrid.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!