Connect with us

LABARAI

RIKICIN APC A ZAMFARA: Kotu Ta Ki Sauraren Karar 

Published

on

Kotun daukaka kara ta dage sauraren shari’ar rikicin APC a Zamfara bayan bangaren da ya shigar da karar ya ce bai yadda da alkalan kotun ba.

Bangaren Sanata Marafa ne ya daukaka kara a Sakkwato domin kalubalantar hukuncin da kotun tarayya a Gusau ta zartar cewa ba a yi zaben fitar da ‘yan takara na jam’iyyar APC a Zamfara.

Barista Misbahu Salahuddin daya daga cikin lauyoyin da ke kare Sanata Marafa ya shaida wa BBC cewa Alkalan kotun daukaka karar ne suka ki sauraren karar.

“Bayan mun hallara a gaban kotu sai magatakarda ya fito ya ce manyan alkalai da aka turo sun ce ba za su zauna ba,” in ji shi.

Karar da aka dage dai na zuwa ne bayan kammala zaben gwamna a Zamfara inda hukumar zabe ta sanar da Muktar Shehu Idris dan takarar bangaren gwamnati a jam’iyyar APC da ake kalubalanta a matsayin wanda ya lashe zaben.

Wata Kotun daukaka kara a Abuja ce ta bai wa hukumar zabe INEC umurnin ta amince da ‘yan takarar APC a Zamfara, bayan da a farko INEC ta ki amincewa da ‘yan takarar jam’iyyar saboda ta gaza yin zaben fitar da ‘yan takara.

Lauyan gwamnati Barista Suraj Gusau ya ce yanzu suna jiran lokacin da za a sake sauraren karar bayan sun halarci zaman kotun daukaka karar a Sakkwato da ba a zauna ba a ranar Laraba.

Bangaren Marafa ya rubuta takarda zuwa ga Alkalin alkalan kotun daukaka kara mai shari’a Zainab Balkachuwa inda suka nemi a a sake alkalan da za su yi shari’ar saboda ba su yadda da wadanda za su saurari karar da suka daukaka ba.

“Yanzu muna jiran sabbin alkalan da za a turo domin sauraren shari’ar,” in ji Lauyan Sanata Marafa, Barista Misbahu.

Wa’adin daukaka karar dai wata biyu ne, kuma yanzu saura kwana 12 ya rage wa’adin karar da Marafa ya daukaka ya cika. Hakan na nufin shari’ar ba za ta wuce kwana 12 ba ke nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!