Connect with us

WASANNI

Ronaldo Bai Yi Kokarin Komai Ba –Simeone

Published

on

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ya bayyana cewa dan wasa Ronaldo bai burge kowa ba saboda ya zura kwallaye uku a ragar kungiyarsa a wasan da suka fafata na cin kofin zakarun turai na ranar Talata.
Cristiano Ronaldo ya ci kwallaye uku rigis wanda hakan ya sa Jubentus ta yi waje da Atletico Madrid, ta kuma kai wasan dab da na kusa dana karshe na gasar cin kofin Zakarun Turai na wannan kakar.
A wasansu na farko a Madrid Atletico ce ta ci Jubentus 2-0, amma reshe ya juye da mujiya a wannan karawa da akayi a Italiya, Jubentus ta rama biyun har ma ta kara kwallo daya wadda ta ba ta nasarar zuwa matakin na gaba da ci 3-2 gida da waje.
Cristiano Ronaldo ya ci kwallon farko ana minti 27 da wasa, sannan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci da minti hudu kacal ya kara ta biyu duka da ka sannan ana saura minti hudu lokaci ya cika na ka’idar minti 90 sai Jubentus ta samu fanareti bayan da Angel Correa ya yi wa Federico Bernardeschi keta, sai dan wasan na Portugal ya buga fanaretin ya ci kuma kwallon da ya ci ta ukun ta kasance kwallo ta 124 kuma karo na takwas da ya ci uku rigis a gasar Zakarun Turai.
Tashi daga wasan ke da wuya sai magoya bayan kungiyar ta Italiya suka barke da sowa, su kuwa ‘yan wasan na Jubentus suka yi kan Ronaldon mai shekara 34 cike da murna amma rashin nasarar ya sa Atletico Madrid ta rasa damar yin wasan karshe na gasar ta Zakarun Turai ta bana a filinta na Wanda Metropolitano ranar 1 ga watan Yuni.
A ranar Juma’a ne za a fitar da jadawalin wasan matakin na dab da na kusa dana karshe, na kungiyoyi takwas da karfe 11 na safe agogon GMT sai dai kungiyar Jubentus itace kawai ta rage a kasar Italiya
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!