Connect with us

KASASHEN WAJE

Sojin Nijeriya Sun Hallaka ‘Yan Bindiga 55 A Garuruwar Dake Kan Iyaka

Published

on

Dakarun rundunar sojin Nijeriya da ke cikin Operation Sharan Daji a Zamfara sun yi nasarar hallaka ‘yan bindiga 55 baya ga kubutar da mutane 760 wadanda ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.
Kamfanin dillancin Labaran Nijeriya NAN, ya ruwaito wata sanarwar rundunar sojin kasar mai dauke da sa hannun daraktan yada labaranta Manjo Janar Clement Abiade na cewa dakarunsu sun kuma yi nasarar kwace tarin makamai a hannun ‘yan bindigar.
Sanarwar ta ce dakarun sojin sun yi wa maboyar ‘yan tawayen kofar rago ne, lamarin da ya hana musu damar tserewa yayin da su kuma suka rika bude musu wuta.
A cewar rundunar yanzu haka ta kame wasu mutane 24 a cikin dajin wadanda aka yi ittifakin ko dai masu kai hare-hare kauyukan jihar ne ko kuma masu garkuwa da mutane, sai dai sanarwar ta ce suna ci gaba da bincike don hukunta su dai dai da laifunsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!